• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Yi  Allah-wadai Da Harin Da Ake Kai Wa ‘Yan Jarida A Gaza, Ta Yi Kira A Gaggauta Tsagaita Wuta 

bySulaiman
2 years ago
Gaza

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi Allah-wadai da harin da sojojin Isra’ila ke kai wa ‘yan jarida a rikicin da ke gudana a ƙasar Falasɗinu, yana mai jaddada cewa, matakin na nuna take haƙƙin ‘yan jarida da kuma haƙƙin ɗan Adam.

A cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Ministan, Rabi’u Ibrahim, ya ce Idris ya bayyana hakan ne a jawabin sa a Taro na Musamman na Ministocin Yaɗa Labarai na Ƙasashen Musulmi mai taken: “Bayar Da Labarin Ƙarya Da Kuma Kisan ‘Yan Jarida Da Gwamnatin Isra’ila ke yi a Lokacin Mamayar da Isra’ila ta yi wa Falasɗinu,” wanda aka gudanar a ranar Asabar, 24 ga Fabrairu, 2024 a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya.

  • Wani Sojan Amurka Ya Bankawa Kansa Wuta Don Nuna Goyon Bayansa Ga Falasdinawa
  • Gobara Ta Ƙone Gidan Ƙaramar Ministar Birnin Tarayya Abuja, Mariya Bunkure

Ministan, wanda ya samu wakilcin Shugaban Ofishin Jakadancin Nijeriya a ƙasar Turkiyya, Ambasada Zayyad Abdul-Salam, ya bayyana cewa tun farkon rikicin, ‘yan jarida na ta fuskantar matsantawa, tsoratarwa da tashin hankali, har ma da kisa saboda kawai suna gudanar da aikin su na sanar da jama’a da kiyaye ƙa’idojin gaskiya da adalci.

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Ya ce: “Daga ƙididdigar da Kwamitin Kare Haƙƙin ‘Yan Jarida na duniya (CPJ) ya bayar, an kashe ‘yan jarida da ma’aikatan kafafen watsa labarai kusan tamanin da takwas tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

“A matsayin mu na Ministocin Yaɗa Labarai da ke wakiltar ƙasashe a Ƙungiyar Ƙasashen Musulunci, ya zama wajibi a gare mu da mu yi Allah-wadai da irin wannan ta’asa da tauye haƙƙin ‘yan jarida da ke gudanar da ayyukan su a Falasɗinu.

“Dole ne mu tsaya tsayin daka don goyon bayan abokan aikin mu na kafafen yaɗa labarai waɗanda suke sadaukar da rayukan su a kullum don bayar da rahoton rikici a Falasɗinu wacce aka mamaye da kuma ba da murya ga marasa murya.”

Idris, wanda ya buƙaci takwarorin sa a ko da yaushe da su dage kan ganin an tabbatar da gaskiya a kowane lokaci ta hanyar neman yanayi mai kyau don bai wa ‘yan jarida damar gudanar da ayyukan su, ya yi tir da duk wani yunƙuri na karkatar da gaskiya tare da rashin bayyana haƙiƙanin halin da mutane ke ciki a Falasɗinu.

Ya shawarci ministocin da ke halartar taron da su binciko dabarun sadarwa, goyon baya, da haɗin gwiwa don faɗaɗa muryar ‘yan jarida waɗanda ke da ƙarfin halin tattara bayanan take haƙƙin bil’adama da cin zarafi da ake yi wa al’ummar Falasɗinu.

Ya ce: “Babban martanin mu dole ne ya kasance sadaukarwa don kiyaye ƙa’idojin ‘yancin ‘yan jarida, ‘yancin faɗin albarkacin baki, da ‘yancin samun bayanai. Waɗannan muhimman haƙƙoƙin ɗan’adam waɗanda ke cikin dokokin ƙasa da ƙasa sun zama ginshiƙan dimokiraɗiyya da kyakkyawan shugabanci.

“Ba za mu ƙyale waɗanda ke neman su murƙushe saɓanin ra’ayi su tattake su kuma su sarrafa labarin ba.”

Ministan ya yi kira da a tsagaita buɗe wuta cikin gaggawa a Gaza kuma ya jaddada matsayin Nijeriya kan samar da ƙasashe biyu don magance rikicin Falasɗinu, da tabbatar da an mutunta haƙƙi da ‘yancin al’ummar Falasɗinu da Isra’ila.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
Manzon Musamman Na Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Jana’izar Marigayi Shugaba Kasar Namibia Hage Geingob

Manzon Musamman Na Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Jana'izar Marigayi Shugaba Kasar Namibia Hage Geingob

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version