Gwamnatin Nijeriya ta yi gagarumar nasara a kotun Ingila wajen sa kotun ta jingine umarnin biyan wani kamfanin kasashen ketare diyyar dala biliyan 11 saboda soke kwangilar da aka ba shi na samar da iskar gas.Â
A shekarar 2010 gwamnatin Nijeriya ta bai wa kamfanin P&ID kwangilar shekaru 20 na ginawa tare da sarrafa iskar gas a sansaninsa da ke kudancin kasar nan, a yunkurin ganin an samu cin gajiyar arzikin makamashin da ake da shi.
- Nijeriya Ta Yi Nasara A Kotun Ingila Kan Rikicinta Da Kamfanin P&ID
- Kwastam Za Ta Rungumi Aiki Da Fasahar Zamani Domin Habaka Harkokinta – Adeniyi
Daga bisani, Nijeriya ta nuna rashin gamsuwarta da aikin kamfanin abin da ya sa ta sanar da soke kwangilar, kuma nan take kamfanin ya ruga kotu a Landan a 2017 domin neman a bi masa hakkinsa.
Kotun da ke birnin Landan ta bada umarnin cewar Nijeriya ta biya kamfanin P&ID dala biliyan shida da miliyan 600 a matsayin asarar da ya yi na ribar aikin, yayin kudin ruwan da ya yi ta karuwa kuma ya sa adadin kudin da za a biya kamfanin ya tashi zuwa sama da dala biliyan 11, kudin da ya zarce kasafin kudin Nijeriya na bangaren kula da lafiyar jama’a na shekarar 2019.
Sai dai lauyoyin Nijeriya sun ce ba a yi wa kasar nan adalci ba wajen wancan hukunci, saboda abin da suka kira bata sunan da kamfanin P&ID ya yi da kuma makudan kudaden da ya bayar a matsayin cin hanci ga wasu manyan jami’an gwamnati domin samun kwangilar tare da bai wa lauyoyin gwamnati cin hanci domin karbar wasu muhimman takardu domin gabatarwa kotun.
Shi dai P&ID ya musanta cewar ya samu kwangilar ce ta hanyar bada cin hanci da kuma musanta bai wa lauyoyin Nijeriya cin hanci domin samun takardun bayanai, inda ya zargi hukumomin kasar da rashin iya aiki a matsayin abin da ya haifar da matsalar da aka soke kwangilar da aka ba shi.
Alkalin kotun, Robin Knowles ya jingine hukuncin biyan kamfanin P&ID diyyar dala biliyan 11 tare da bai wa Nijeriya damar kalubalantar hukuncin da aka yi a baya lokacin gabatar da na shi hukuncin a ranar Litinin, yayin da ya tabbatar da cewar an samar da wannan kwangilar da ake takaddama a kai ne ta haramcaciyar hanyar da ta sabawa manufofin jama’a.