Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na kara bunkasa noman Rogo domin samar wa masana’antu da kuma fitarwa zuwa waje.
Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar gwamnatin tarayya da ke gudanar da bincike kan masana’antu (FIIRO) da ke garin Oshodi a Jihar Legas.
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
- Uwargidan Shugaban Kasa Ta Bude Makaranta Ga Matan Da Aka Kora A Manyan Makarantu A Bauchi
Darakta Janar ta cibiyar, Jummai Tutuwa ce ta zagaya da ministan cikin sassan cibiyar baki-daya, don gane wa idonsa.
Har ila yau, bayan kammala ziyarar, ministan ya kuma koka a kan rashin kula da injinan sarrafa rogon da ke cikin hukumar.
Sannan ya sanar da cewa, idan har ana bai wa injinan sarrafa Rogon kulawar da ta dace, hakan zai taimaka wajen kara bunkasa noman Rogon tare da kara samar da ayyukan yi a fadin wannan kasa baki-daya.
“Muna da injinan sarrafa Rogo a wannan cibiya, wadanda za a iya amfani da su wajen kara habaka sarrafa Rogon, wanda hakan zai bai wa wannan kasa damar kara sarrafa shi daga tan miliyan 64 zuwa tan miliyan 120 a duk shekara”, a cewar Nnaji.
Kazalika ya kara da cewa, ma’aikatarsa za ta yi dukkanin mai yiwuwa; don ganin ta taimaka wa cibiyar domin amfana da kimiyyar zamani, wanda hakan zai ba ta damar karfafa sarrafa Rogo zuwa Fulawar da za a rinka fitar da ita zuwa kasashen ketare tare da kuma kara samar da wadataccen abinci a fadin Nijeriya baki-daya.
Haka zalika ministan ya bayyana cewa, “Nan ba da jimawa ba; za mu fara sarrafa abin da muke bukata a cikin wannan kasa ba tare da mun yi amfani amfani da Dalar Amurka, don shigo da kaya daga kasashen waje ba”.
Ya kara da cewa, “Daya daga cikin abin da muka mayar da hankali a kai shi ne; fara yin shuka ta hanyar gwaji, domin samar da Rogon da dama tare da samar da ganyen Filanten, don sarrafa shi zuwa Takarda” .
A nata jawabin tun da farko, Darakta Janar ta cibiyar; Jummai Tutuwa, ta sheda wa ministan kokarin da cibiyar ta ke yi don tabbatar da sarrafa abinci tare da wadatuwarsa a fadin kasar nan, inda ta kara da cewa, cibiyar na da karfin samar da Tumatir da Rogon da za a sarrafa zuwa Biredi da kuma Filanten.