• English
  • Business News
Wednesday, August 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai

by Sulaiman
6 months ago
in Labarai
0
Yajin aiki
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da yarjejeniyoyin fahimtar juna guda biyu da aka rattaba wa hannu tsakanin Hukumar Watsa Labarai ta ƙasar Sin (China Media Group) da Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) a Taron Haɗin Gwiwa tsakanin Sin da Afrika (FOCAC) wanda aka gudanar a birnin Beijing.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya tabbatar da hakan yayin da ya karɓi jakadan Chana a Nijeriya, Mista Yu Dunhai, a wata ziyarar ban-girma da ya kai masa a ofishin sa ranar Alhamis.

  • Kasar Sin A Matsayin Katafariyar Cibiyar Kere-Keren Mutum-Mutumi A Duniya
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 92, Sun Kubutar Da Mutane 75 A Cikin Mako Guda – DHQ

Ya bayyana cewa yarjejeniyoyin za su ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta fuskar kafofin watsa labarai da sadarwa.

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 8 A Kaduna, Sun Jikkata Wasu

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 5 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan.

“NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da tashoshi sama da ɗari a faɗin ƙasar nan, tana isar da shirye-shiryen ta ga sama da mutane miliyan 200.

“Hakan ya sa muke da buƙatar amfani da wannan haɗin gwiwa don musayar bayanai da fasaha, tare da amfana da juna.”

Ministan ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun haɗa da musayar bayanai, shirye-shirye, da fasaha domin inganta ayyukan gidajen watsa labarai na Nijeriya tare da ƙarfafa aikin jarida bisa kyawawan ƙa’idojin duniya.

Haka nan, ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa da Chana domin yaƙi da labaran ƙarya da yaudara ta hanyar yaɗa bayanai marasa tushe.

Ya ce: “Labaran ƙarya da yaudara manyan barazana ne ga duniya. Mun san cewa ƙasar Chana tana da matuƙar damuwa game da wannan batu, haka nan kuma Nijeriya.

“Wannan ba matsala ce da ta shafi ƙasashen mu biyu kawai ba, matsala ce ta duniya baki ɗaya. Saboda haka, muna son yin aiki tare da ƙasar Chana domin yaƙi da labaran bogi da yaɗa ingantattun bayanai da za su amfani al’umma.”

Idris ya tabbatar wa jakaden na Chana cewa Nijeriya na kiyaye ‘yancin ‘yan jarida, wanda wani muhimmin ɓangare ne na jajircewar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya.

Ya ce: “A Nijeriya, ‘yan jarida suna da ‘yancin aikin su. Duk da yake akwai matsaloli a wasu lokuta, muna aiki a kai a kai domin gyara su. Nijeriya tana da ‘yancin watsa labarai mai yawa, kuma muna son ci gaba da hakan.”

Har ila yau, ya buƙaci kamfanonin ƙasar Chana da su yi amfani da damar da manufofin Tinubu ke samarwa wajen zuba jari a Nijeriya.

A nasa jawabin, Jakada Yu Dunhai ya jaddada aniyar sa ta ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da Chana, tare da yaba wa Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Ƙasa Tinubu.

Ya ce: “Ina da sa’a sosai kasancewa jakada a lokacin da Shugaban Ƙasa Tinubu yake aiwatar da Ajandar Sabunta Fata don ƙarfafa Nijeriya. Haka nan, a ƙasar Chana, Shugaba Xi Jinping yana jagorantar ƙasar zuwa cigaba ta hanyar sauye-sauyen zamani na ƙasar Chana.”

Jakaden ya bayyana cewa a taron FOCAC da ya gabata a Beijing, Shugabannin Nijeriya da Chana sun amince da ɗaukaka alaƙar ƙasashen zuwa matakin haɗin gwiwar dabarun cigaba.

Haka nan, ya nuna muhimmancin aiwatar da yarjejeniyoyin tsakanin NTA, FRCN, da China Media Group, yana mai cewa kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma.

Ya kuma yaba da yadda kafofin watsa labarai na Nijeriya ke gudanar da ayyukan su bisa gaskiya, daidaito, da riƙon amana.

A ɓangaren zuba jari, jakaden ya bayyana cewa Shugaba Xi Jinping ya ware dala biliyan 50 ($50bn) domin zuba jari a Afrika cikin shekaru uku masu zuwa a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyoyin da aka cimma a taron FOCAC.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Bai Wa Sojoji Haɗin Kai 

Next Post

Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna

Related

Mazauna Kuyello A Jihar Kaduna Na Cikin Zullumin Bayyanar ‘Yan Ta’addar Ansaru
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 8 A Kaduna, Sun Jikkata Wasu

2 hours ago
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba
Labarai

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 5 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

4 hours ago
Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba
Manyan Labarai

NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi 

4 hours ago
PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro
Manyan Labarai

PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro

6 hours ago
Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar
Manyan Labarai

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

7 hours ago
Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Labarai

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

15 hours ago
Next Post
Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna

Bukatar Kafa Dokar-ta-baci Kan Yaduwar Jabun Magunguna

LABARAI MASU NASABA

Mazauna Kuyello A Jihar Kaduna Na Cikin Zullumin Bayyanar ‘Yan Ta’addar Ansaru

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 8 A Kaduna, Sun Jikkata Wasu

August 27, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 5 Da Aka Sace A Jihar Kebbi

August 27, 2025
Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba

NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi 

August 27, 2025
PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro

PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro

August 27, 2025
Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

August 27, 2025
Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya

August 26, 2025
Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

Shin Mummunan Halin Da Aka Shiga Yayin Yakin Duniya Na II Bai Isa Darasi Ba?

August 26, 2025
Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Dashen Bishiyoyi Na 2025

August 26, 2025
Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi

August 26, 2025
Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin

Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna

August 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.