Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Malam Mele Kyari ya yi has ashen cewa Nijeriya za ta fara fitar da tatancen man fetur zuwa kasashen ketare a 2024.
Shugaban kamfanin NNPCL ya bayyana hakan ne a ranar Litinin wajen taron kungiyar manyan ma’aikatan gas da fetur na Nijeriya (PENGASSAN) da aka gudanar Abuja, inda ya ce ba da jimawa ba kasar nan za ta zama mai dogaro da kanta wajen samar da kayayyaki.
Kyari ya bayar da dalilan da ya sa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, inda ya kara da ce idan ba a cire ba, to da kamfanin NNPCL ya talauce.
Ya ce Nijeriya na bukatar samun makamashi mai dorewa wanda aka dora kan albarkatun da ake da su da kuma maye gurbin wanda aka rasa.
“A yau, muna fitar da kashi 100 na abin da muke nomawa, babu wata kasa mai dogaro da kanta take haka, don haka ne ya zama wajibi mu cika aikinmu.
“Haka muke fatan mu gani. Ba na son yin magana game da lamarin. Mun gaji da magana game da shi. Amma abin da ya kamata mu cimma shi ne, dole ne kasar nan ta kasance mai fitar da albarkatun man fetur.
“Ina mai tabbatar da cewa a shekarar 2024, kasar nan za ta fara fitar da albarkatun man fetur. Ma’anar wannan ita ce, za mu samu isassun man fetur cikin kasar nan, idan aka tace a cikin gida, muna da damarmaki mai yawan gaske, samun dukiya, samun haraji, da duk wani nau’in mai haka da haka, samar da ayyukan yi da dai sauransu,” in ji shi.
Tun da farko, shugaban kungiyar PENGASSAN, Kwamared Festus Osifo, ya yi kira da a daidaita albashin ma’aikatan mai da na iskar gas a kasar nan.