Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su guji goyon bayan jam’iyyar APC a dukkan zabukan 2023.
Gwamnan ya yi gargadin cewa kasar za ta wargajewa idan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
- Sin Na Da Aniyar Cimma Nasarar Yaki Da Cin Hanci Da Karbar Rashawa
- ‘Yan Fasakwari Sun Harbe Jami’in Kwastam, Sun Raunata Uku A Kwara
Obaseki ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a Jihar Edo.
Gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba bashin da ake bin Nijeriya zai kai Naira tiriliyan 60, lamarin da zai shafi rayuwa marasa karfi.
“Ya kamata mu duba kawunanmu a matsayin ‘yan kasa idan muka yi tunanin zabar gwamnati irin ta APC, to mu san me zai je ya dawo.
“Kamar yadda na fada, matukar APC ta hau mulki. Wannan kasa za ta iya wargajewa.”
Obaseki ya jaddada cewa “babu wanda ya yi irin barnar da gwamnatin APC ta yi”.
Gwamnan ya shaida wa ‘yan jam’iyyar da magoya bayansa cewa bai san yadda al’ummar kasar za ta farfado ba.
Obaseki ya ce bai zai huts ba, har sai zuwa lokacin da Atiku Abubakar na PDP ya yi nasara, “ba za mu iya yin barcin dare da na rana ba.
“Bashin Nijeriya zai kai Naira tiriliyan 60. Yaushe zamu fita daga cikin wannan hali?
“Kowace rana, kowane wata ba su da aiki sai buga kudi. Lokacin da na yi magana fiye da shekara guda da ta wuce, ban san abun zai yi muni kamar wannan lokacin ba.
“Me zai faru da Naira, Allah ne kadai zai taimake mu. Sun lalata ko ina a kasar nan,” in ji shi.