Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na mayar da Nijeriya matsayin jagora a harkokin noma cikin kasashen duniya nan da shekarar 2025.
Da yake jawabi a wurin taron kudu maso kudu na ajandar sake fata a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasa ya kaddamar da ayyukan samar da aikin noma, wani gagarumin shiri da nufin kawo sauyi a fannin noma a Nijeriya.
- Nijeriya Da Brazil Sun Cimma Yarjejeniyar Bunkasa Noman Zamani A Kasar Nan
- Gwamnatin Tinubu Na Amfani Da Kuɗaɗen Tallafin Mai Don Ci Gaban Al’umma – Minista
“Wannan aikin wata sanarwa ce mai karfi cewa mun kuduri aniyar mayar da albarkatun da ba na man fetur ba zuwa wadata na gama gari,” in ji Tinubu.
Ya kuma jaddada cewa yankin kudu maso kudu, wanda ya shahara da dimbin albarkatun kasa, zai taka rawar gani wajen tafiyar da sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya fiye da man fetur da iskar gas.
Sabon shirin da aka kaddamar zai mayar da hankali ne kan sauya fasalin Nijeriya daga noma zuwa ingantaccen tattalin arziki wajen fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje. A cewar Tinubu, an tsara aikin ne domin magance matsalar abinci tare da samar da damammaki na tattalin arziki ga miliyoyin ‘yan Nijeriya.
“Burinmu a fili yake. Nan da shekarar 2025, za mu sanya Nijeriya a matsayin babbar kasa wajen fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje,” in ji Tinubu, inda ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ba da goyon bayan da ya dace don tabbatar da nasarar aikin.
Shugaban ya yi nuni da irin damarmakin da yankin kudu maso kudu yake da shi, inda ya bayyana shi a matsayin wata cibiya ta albarkatun da ba a yi amfani da su ba da kuma hazakar Dan’adam.
Ya ce bayan albarkatun man fetur da iskar gas, yankin na da wadatar filaye mai albarka na noma.