Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet), ta yi hasashen samun ruwan sama mai yawa, sannan da yiwuwar ambaliya a wasu sassa na Nijeriya daga Litinin zuwa Laraba.
Jihohin Arewa kamar Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa da Bauchi na iya fuskantar ambaliya.
- An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
- Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
A Arewa ta Tsakiya kuma, Abuja, Filato da Nasarawa za su fuskanci ruwan sama.mai ƙarfi.
A Kudu kuwa, ana sa ran samum ruwan sama mai ƙarfi a jihohin Ribas, Kuros Riba, Delta da Akwa Ibom.
NiMet ta shawarci jama’a da su guji tuƙi a lokacin da ake yin ruwan sama mai ƙarfi, su zauna cikin gida.
Sannan su ɗaure kayan da iska za iya ɗauka.
Ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi kafin tashi.