Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen samun hasken rana da gajimare daga ranar Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.
An fitar da hasashen yanayi na NiMet a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja ya yi hasashen yanayin rana a ranar Litinin tare da gajimare a yankin Arewa tare da yiwuwar samun tsawa da safe a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Sokoto, Zamfara, Kebbi da Kaduna.
- Za A Tafka Mamakon Ruwan Sama A Arewa A Kwanaki Masu Zuwa —NiMet
- Akwai Yiwuwar Afkuwar Wata Sabuwar Ambaliyar Ruwa A Wasu Jihohi – NiMet
A cewar hukumar, ana iya samun tsawa a wasu sassan jihohin Kaduna, Taraba, Adamawa, Bauchi, Gombe, Katsina, Borno, Yobe da kuma Kano.
“An yi hasashen yanayin samun hasken rana a yankin Arewa ta tsakiya tare da yuyuwar samun ruwan sama a sassan babban birnin tarayya da jihohin Neja.
“A washegari, ana hasashen tsawa tare da samun ruwan sama na tsaka-tsaki a wasu sassan babban birnin tarayya, Filato, Kogi, Nasarawa da kuma Binuwai.
“An yi hasashen samun yanayi mai cike da hadari a jihohin kudancin Kudu da kuma garuruwan da ke bakin teku da hasashen samun ruwan sama a sassan Oyo, Ondo, Ogun, Edo, Delta, Cross River, Akwa Ibom, Ribas da Bayelsa,” in ji ta.
Ana kuma hasashen samun tsawa da ruwan sama na tsaka-tsaki a duk yankin nan gaba da rana.
Kamar yadda kafar yada labarai ta NiMet ta ruwaito, ana sa ran zazzafar rana tare da gizagizai a yankin Arewa a ranar Talata, inda ake sa ran za a yi tsawa mai karfin gaske a sassan jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Taraba da Adamawa.
“An yi hasashen yanayin iska tare da tazarar rana a yankin Arewa ta tsakiya tare da yiwuwar samun ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Plateau, Benue, Niger da Kwara.
“Bayan da rana, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama na tsaka-tsaki a yawancin yankin.
“Ana sa ran sararin za ta yi wasai a jihohin kudancin Kudu da kuma jihohin bakin teku tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama na tsaka-tsaki a kan wadannan yankuna,” in ji ta.