Hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) tare da haɗin gwiwar Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke yaƙi da shan miyagun ƙwayori da aikata laifuka (UNODC) sun gabatar da rahoton binciken da suka yi a kan ‘yan Nijeriya da ke kwarara zuwa ƙasashen ƙetare.
Rahoton da aka yi masa laƙabi da SOM an ƙaddamar da shi ne a shelkwatan NIS da ke Abuja a ranar Talata.
Da yake gabatar da jawabin maraba, shugaban hukumar NIS, CGI, Idris Isa Jere ya bayyana cewa duk wani bincike yana da sakamakon. Don haka suka ƙaddamar da wannan rahoton wanda yake buƙatar ɗaukan mataki bayan an kammala nazari tare da yin aiki da shi.
CGI Isah Jere, wanda ya samu wakilcin DCG Haliru ya jinjina wa UNODC bisa gudanar da kyakkyawan aiki na samun nasarar bankaɗo yawan ‘yan Nijeriya da ke yin hijira zuwa ƙasashen ƙetare ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, hukumarsa za ta yi aiki da wannan rahoton wajen yaƙi da safarar ‘yan Nijeriya zuwa ƙasashen ƙetare. Sannan ya yi kira da dukkan jami’an hukumar NIS da su gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada.
A nasa jawabin, wakilin UNODC, Oliver Stolpe ya bayyana cewa an gudanar da wannan bincike ne domin samun nasarar daƙile safarar mutane ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce wannan rahoton zai taimaka wa ƙasashe wajen toshe ɓarnar safarar mutane ta mummunar hanya.
Ya ƙara da cewa UNODC tana ƙoƙarin taimaka wa mambobin ƙasashe da ke cikin Majalisar Ɗinkin Duniya wajen hana safarar mutane ba bisa ƙa’ida ba, wanda zai haddasa haɗin kai a tsakanin ƙasa da ƙasa wajen gudanar da sintirin yaƙi da safarar mutane.
Ya ce wannan bincike ba zai taɓa samun nasara ba sai da haɗin gwiwar shugabancin hukumar NIS da gwamnatin ƙasashen Kanada da Danmak wajen bayar da kuɗaɗe domin samun nasara.
Wakilin ya ce binciken ya samar da alƙamuman yawan ‘yan Nijeriya da ke karara zuwa ƙasashen waje domin faɗakar da gwamnatin Nijeriya da sarakuna da malaman addinai da dukkkan sauran al’umma.
Ya ce ‘yan Nijeriya ne suka fi yin balaguro zuwa ƙasashen Turai da Asiya a tsakanin ƙasashen yammacin Afirka. Ya ƙara da cewa sun haɗa kai ne da hukumar NIS da sauran hukumomi da ƙungiyoyin fararen hula domin yaƙi da safarar ‘yan Nijeriya ta mummunar hanya.
Shi ma ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana cewa safarar mutane ba bisa ƙa’ida ya zama ruwan dare a cikin al’umma saboda matsalolin tattalin arziki, wanda ke sauya asalin ɗabi’un al’umma. Ministan wanda ya samu wakilcin babbar jami’an ma’aikatan harkokin cikin gida Atiruke Ajiboye. Ya ce yana gode wa dukkan waɗanda suka bayar da goyon baya har wannan rahoton ya kammala na safarar mutane ba bisa ƙa’ida ba.
Ya nuna farin cikinsa game da wannan shirin da zai tsaftace al’umma wajen faɗakar da mutane illar safarar mutane domin ceto rayukansu.
Rahoton na NIS da UNODC zai bude sabon babi na bullo da sabbin hanyoyin dakile safarar mutane ba bisa ka’ida ba