Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Jihar Ribas (NIS) James Sunday, ya yi wa manema labarai karin haske kan fara aikin “Operation Tsaron Iyaka” a Jihar Ribas.
Kwanturolan ya ce hakan ya samo asali ne daga ganawar da suka yi a jihar Akwa Ibom da mukaddashiyar kwanturola Janar ta Hukumar Shige da Fice, Caroline Wuraola Adepoju wadda ta kai ziyarar aiki ta kwanaki 2 a Akwa Ibom kuma ta ziyarci ofishin kula da iyakoki na ruwa a jihar.
Sauran manyan jami’ai masu mukamin Kwanturola na Shiyyar E na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya na cikin tawagarta, musamman Kwanturola Akwa Ibom, Abia, Cross River, Ebonyi, Rivers da na Sashen Kula da Iyaka ta Ruwa da ke Jihar Akwa Ibom.
An yi ziyarar ce domin tantance ayyukan bakin iyaka, ayyuka da ayyukan tattalin arziki da aka gudanar a jihar Rivers kasancewar jihar a gabar ruwa.
Kwanturola James Sunday, ya ce “Operation Tsaron Iyaka” wanda ke nuni da karfafa tsaron kan iyaka shi ne abin da zai fi mayar da hankali a kai sakamakon taron da suka yi da kuma amfani da umarnin da mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice Caroline Wuraola Adepoju ta bayar, shi ya sa na yanke shawarar fara aikin tare da jami’anmu a Jihar Ribas.
“Jami’amu za su kai samame a wurare da maboya da tashar jiragen ruwa inda ake zargin ‘yan kasar waje da suka shigo Nijeriya ba bisa ka’ida ba suna boye a nan, tare da cafke su da gurfanar da duk wani mutum ko rukuni na bakin haure da aka gano suna zaune ba tare da ingantattun takardu na shigowa ba.
“Za mu bazama aiki a wannan yunkuri na kawar da ‘yan ci-rani ba bisa ka’ida ba a Jihar Ribas wadanda za su iya shiga aikata cikin munanan ayyuka tare da gujewa gano su a duk lokacin da suka aikata wani laifi ko kuma suka shiga cikin wani abu mara kyau wanda na iya kaiwa ga rashin tsaro ga rayuwa da dukiyoyin mutane a Ribas.” In ji shi.
Sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na reshen hukumar ta NIS da ke JIhar Ribas, ASI Nwosu Chukwu ya fitar, ta kara da cewa hukumar ta fara aiki nan take, kuma za ta ci gaba da aiki har sai ta gamsu da cewa ‘yan ci-rani ba bisa ka’ida ba sun tafi da kansu wuraren da suka kamata domin tsara takardunsu da kuma al’ummarsu ta bin ka’idar ECOWAS da sauran su, da aka shimfida bisa tanade-tanade na Dokar Shige da Fice ta 2015 da Dokokin 2017 da sauran manyan dokokin kasar.
Kwanturola James ya ba da tabbacin masu bin doka da oda daa cikin ‘yan ci-ranin a kullum suna ba su kariya da harkokin kasuwancinsu da rayuwarsu da dukiyoyinsu a Ribas sannan ya shawarci al’umma ko shugabannin kungiyoyi da su fito da jerin sunayen mambobinsu na jihar Ribas domin tabbatar da cewa kowa ya yi rajistar da ta kamata a hukumar ta Shige da Fice (NIS).