Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), reshen Jihar Ribas ta nanata bukatar kamfanoni da kungiyoyi su mutunta Dokar Bangaren Zartarwa kan ayyukan Injiniya don bai wa ‘yan Nijeriya isassun ayyukan yi ta yadda za a tabbatar da cewa wadanda ba ‘yan Nijeriya ba, ba su shiga ayyukan da aka san akwai kwararrun ‘yan Nijeriya da za su iya gudanarwa ba.
A cewar NIS, Dokar mai taken ‘Executive Order Five’ da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a shekarar 2018, ta kudiri aniyar bunkasa kimiyya, fasahar kere-kere da kuma shigar da kamfanonin cikin gida a ayyukan gwamnati da suka hada da daben zamani na Tiling da Interlocks da jera bulolluka na gini da dai sauransu wadanda aka tabbatar da cewa ‘yan kasa za su iya yin aiki mai kyau kuma daidai wajen gudanar da su.
A wata tattaunawa da Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa reshen Jihar Ribas, CIS James Sunday, ranar Alhamis, a yayin da rundunar take shirin gudanar da taron kwana daya da masu ruwa da tsaki da kamfanonin da suka amince da bayar da kaso na ‘yan kasashen ketare, ya bayyana cewa NIS ta dukufa wajen tabbatar da ganin ana bin ka’ida a bangaren bayar da izinin kasuwanci da kuma daukar ma’aikata da sauran harkokin zuba jari da suke da nasaba da hukumar tasu ta shige da fice.
Sama da kamfanoni dari ne ake sa ran za su halarci taron bitar na yini guda a garin Fatakwal na jihar Ribas.
Ya kuma yi nuni da cewa, dole ne a takaita wuraren da ‘yan kasar waje ke aiki da aka tabbatar akwai ‘yan Nijeriya da za su iya yi kamar yadda Dokar Zartaswa a bangaren aikin Injiniya ta tanada kuma a ba su cikakkiyar dama ba tare da wata shakka ba don sanya ‘yan Nijeriya su ci gajiyar wuraren aiki a Nijeriya, ta yadda za a rage masu sha’awar fita waje neman aikin musamman matasa masu neman aikin yi domin bunkasa walwalar rayuwarsu.
…Manyan Kalubalen Da Sabbin Shugabannin Majalisa Za Su Iya Fuskanta