Hukumar Shige da Fice ta Kasa reshen Jihar Ribas ta yi wa jami’anta da suka samu Karin girma ado da sabbin mukamansu a shalkwatarta da ke titin Aba tare da kaddamar da sabbin jami’ai 54 da aka dauka aiki.
Daga cikin wadanda aka yi wa ado da sabbin mukaman, akwai manya da matsakaitan jami’ai 98, da suka kunshi jami’ai mata 43 da maza 55.
Sanarwar da ta fito daga bakin ACG, James Sunday, ta bayyana cewa bikin ya samu halartar iyalan sabbin jami’an da aka dauka da ‘yan’uwa da abokan arzikin manyan jami’an da aka kara musu girma.
NIS reshen jihar ta Ribas ta yi amfani da wannan damar wajen gode wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, da Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo da sauran mambobin Hukumar Gudanarwa ta CDCFIB, da Kwanturola Janar ta NIS, Caroline Wuraola Adepoju da sauran manyan mahukuntan hukumar, bisa Karin girman da aka yi.
Ta ce Karin girman abu ne da zai kara walwala da kwarin gwiwar ci gaba da aiki tukuru a tsakanin jami’an hukumar, musamman bisa yadda ake cewa duk wanda aka yi wa alheri za a nemi ya kara azama kan abin da yake yi.
Hukumar ta NIS reshen Ribas ta jaddada cewa jami’anta a shirye suke su kara kaimi kan ayyukan da aka ba su damar gudanarwa bisa doka, kana ta yi fatan samun Karin nasara a sabuwar shekara mai zuwa da ake dab da shiga.