Babban Ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) mai kula da Shiyya ta Uku (Zone C) da ke da shalkwata a Bauchi, ya kaddamar ma da wani aiki mai lakabin “Operation Tsaron Iyaka”, jim kadan bayan babban jami’in shiyya na hukumar, ACG James Sunday yak ama aiki.
An gudanar da taro a tsakanin babban jami’in da kwanturololin NIS da ke jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Filato da kuma Yobe da nufin karfafa ayyukan jami’an shige da fice a shiyyar arewa maso gabas da Filato.
Kamar yadda ACG James Sunday ya yi wa LEADERSHIP Hausa bayani, sun bullo da tsarin aikin ne bisa irin hobbasar da shugabar hukumar ta NIS, Caroline Wuaola Adepoju da Ministan Cikin Gida, Tunji Ojo suke yi a kan tsaron iyaka, “kuma shi ya sa jami’anmu suka mike haikan don sauke nauyin da ke wuyansu, shi ya sa muka gudanar da taron a Gombe ba a shalkwatarmu ta Bauchi ba.”
Da yake Karin haske kan dalilin bullo da aikin, ACG James Sunday ya ce, “A matsayina na Babban Jami’in Shiyya, an kawo ni ne don na yi aiki tukuru ba na zauna a ofis ba, wajibi ne kwamandojinmu da sauran jami’anmu su nuna shugabanci nagari da kansu ba sako ba domin karfafa gwiwar jami’ai. Ina da manyan ofishoshin jihohi guda shida a karkashina ciki har da shalkwatar shiyyar da kanta, tare da jami’ai dubu 3,081 a karkashin kulawata. Ba zan iya barinsu ba tare da fuskantar wata alkibla ba da kyakkyawan jagoranci a wannan aiki da Allah ya ba mu amanarsa a kasarmu.
“Ba za mu iya kunyata kasarmu ba da kuma amanar da aka ba mu ta aiki wurin tabbatar da cewa muna aiki da kwarewa bisa bin doka da kuma kare tsaron kasa. Don haka inaw a dukkan kwanturololi barka da zuwa tare da ba su tabbacin cewa mun bullo da wannan aiki ne saboda samun nasara da kara kare martabar aikinmu wanda za mu cimma burin haka bisa tabbacin da muke samu daga kwanturololin jihohi.”
ACG James Sunday, ya bayyana cewa taron nasu ya kudiri aniyar waiwaye game da tarihin ayyukan NIS da kuma la’akari da tsarin gudanar da tsaron Nijeriya domin su lalubo bakin zaren tabbatar da tsaron iyaka a yankin arewa maso gabas da kuma Filato.
Ya kara da cewa a wannan lokacin, ‘yan ta’adda da masu sace mutane suna garkuwa da su na kokarin mayar da tsarin tsaron Nijeriya abin dariya da ba’a wanda ta hanyar hakan jami’ai masu kwazon aiki sun rasa rayukansu, haka nan ‘yan kasa nagari tare da asarar tarin dukiyoyi.
“Wadannan miyagu suna tafka ta’asa ta hanyar sace-sacen mutane don karbar kudin fansa kuma su kashe wadanda suka kama. Wannan ya kamata ya zama kalubale ga duk wani kwamanda da aka tura aikin tsaron rayuka da dukiyoyi domin sauya irin rayuwar da al’umma ke yi yanzu. Ya kamata a sauya tsarin gudanar da aiki domin mayar da martini kan shaidancin da miyagun nan ke yi da ke barazana ga al’umma da kuma gudanar da shugabanci nagari. Wannan yana daga cikin kudurorina na aiki a wannan shiyya.
“Taronmu na yau ba zai iya warware dukkan abubuwan da suka shafi tsaro da ke nasaba da aikin NIS ba nak are iyakokin kasa da kula da shige da ficen mutane, amma tabbas zai ba da dama a shawo kan wasu matsaloli da suka shafi iyakoki da shige da fice a arewa maso gabas da Filato wanda ni da sauran kwanturololin jihohin wannan shiyya cikin taimakon Allah za mu yi tsayin daka wajen aiwatarwa daidai da tsarin ayyuka na NIS a fadin kasa a karkashin jagorancin Kwanturola Janar Caroline Wuraola Adepoju.
“Rahotonmu na wannan taron ba zai tafi a banza ba ko a jefa a kwandon shara saboda abubuwan da za a bullo da sun a basirar aiki, babban burinmu shi ne tabbatar da tsaron iyaka a arewa maso gabas, mun matsa kaimi fiye da lokutan baya ta hanyar aiki da sauran hukumomin tsaro domin kyautata yanayin rayuwar al’ummar kasa. A yau mun samu damar kai ziyara ta musamman ga Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahya wanda mataimakinsa, Dakta Manassah Daniel Jatau ya wakilta, mun bayyana masa dalilin haduwarmu a jihar nan wanda ya yi lale marhabin da shi. Muna fata Allah ya ci gaba da daukaka darajar kasarmu baki daya.” In ji shi