Mukaddashiyar Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), Caroline Wuraola Adepoju, ta amince da sake tura jami’an kula da fasfo fiye da 12 aiki nan take, a wani yunkuri na inganta aikin samar da fasfo da ake yi.
Wannan mataki na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Kenneth Kure ya fitar a ranar Laraba.
- Sojoji Sun Yi Wa ‘Yan Fashin Daji Luguden Wuta, Sun Kashe 22 A Katsina
- Wasu Matasa Sun Kone Ofishin Jakadancin Sweden A Iraki Kan Kona Alkur’ani Mai Tsarki
Wannan wani yunkurin hukumar NIS na inganta tsarin samar da fasfo a ofishin jakadancin Nijeriya a kasashen waje.
Ta ba da tabbacin cewa manyan jami’an da aike manyan ofisoshin hukumar za su samar da tsari mai tasiri da zai inganta hulda tsakanin hukumar da kwastomominta.
Cikin takardar da ya sanya wa hannu, Mataimakin Kwanturola Janar mai kula da harkokin ma’aikata, Usman Babangida, ya bayyana ofisoshin da abin shafa kamar Alausa da Festac da ke Legas, Edo, Anambra, Bayelsa, Kogi, Nassarawa, Filato, Enugu, Abiya, Kano, Taraba, Ondo da dai sauransu.
Adepoju ta umarci dukkan jami’an da aka tura da suna kwarewa wajen warware matsaloli da suka dabaibaye ofisoshin hukumar a jihohin da aka zayyana.
Ta jaddada muhimmancin aikin ga jami’an da aka tura jihohin.
Kazalika, ta bayyana cewa daga yanzu hazikan jami’an hukumar kadai za ake turawa wurare masu muhimmanci don warware matsalolin da suka shafi jama’a.