Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) reshen jihar Bayelsa ta gano wasu sabbin dabarun da masu safarar mutane ke amfani da su wajen domin kauce wa binciken hukumomin tsaro.
Hukumar ta ce, yanzu ta gano masu safarar na amfani da shaidar tafiye-tafiye na ECOWAS (ETC) a matsayin takardun tafiye-tafiyen don fitar da wasu da ake son yin safaransu da basu da wani alaka da ECOWAS domin kauce wa dukkanin binciken hukumomin tsaro don shigar da su kasashen da suke so.
A wata sanarwar da Jami’in watsa labarai na NIS reshen Bayelsa ya fitar a yau Alhamis, ya ce, wannan matakin ya biyo bayan kokarin da Kwanturolan hukumar reshen jihar Bayelsa James Sunday ke yi wajen ganin an fitar da tsare-tsaren da suka dace wajen dakile masu safaran mutane.
Hukumar ta nuna damuwarta kan yadda ake samun matasa na amfani da shaidar ECOWAS wajen yin safaran, “Kan hakan an umarci sashin da ke kula da ECOWAS da su kara zurfafa bincike wajen gano takardun masu amfani da shaidar ECOWAS domin zurfafa bincike da gano masu mummunar aniya.”
Sanarwar ta ce bayan samun umarnin zurfafa bincike a kalla mutane biyu da ake kokarin safararar su ne aka ceto kana ta wajen daya daga cikinsu ne aka samu bayanin suna amfani da takardun don yin safaran ta barauniyar hanya.
Hukumar ta ce ba za su yi kasa a guiwa ba za su Kara himma da azama wajen dakile masu safaran mutane ta hanyar fadada bincike da amfani da hanyoyin zamani wajen dakile lamarin.
Hukumar ta NIS ta nemi iyaye da su kara kula da ‘ya’yansu kana su daina barinsu tare da mutanen da za su boyesu, kazalika sun nemi hadin kai jama’a wajen samar musu da bayanai na duk wani da suke zargi domin daukan matakan da suka dace cikin gaggawa.