Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta kasa (NIS) ta ayyana cewa jami’anta sun cafke wasu mutane da ake zargin dillalan makamai ne a kan iyakar a Mfum da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru.
Garin Mfum wanda yake karamar hukumar Ikom a Jihar Kuros Riba ya kasance cibiyar kasuwanci da ‘yan kasuwa na duniya ke yada zango yayin da suke safarar kayan abinci , man fetur da sauransu ta motoci zuwa kasar Kamaru.
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
- 2023: Lawan Da Akpabio Ba Su Cikin ‘Yan Takarar Sanata – INEC
Kwanturolan NIS mai kula da iyakar kasa ta Mfum, CI Ndubuisi Eneregbu ya yi bayanin cafke mutanen a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi .
Eneregbu ya bayyana cewa mutum uku da aka cafke sun hada da ‘Yan Nijeriya biyu da kuma wani bakonhaure dan Kamaru wanda ya amsa cewa shi mamba ne na kungiyar ‘yan aware ta Ambazonia. An dai cafke su ne a kan babura dauke da bindigogi da albarusai.
“An cafke mutanen da ake zargin ne dauke da wata jaka da aka sa kananan bindigogi biyu da albarusai guda uku da wasu kayan tsafi da kuma waya kirar TECNO.
“An mika mutanen da makaman da aka cafke su da su ga ofishin ‘yansanda na yankin Etung domin ci gaba da bincike. Dangane da kokarin da NIS take yi na tsaurara tsaron iyakokin kasa kuwa, Kwanturolan ya ce hukumar ta kirkiro da gudanar da taro a kai a kai tare da sarakunan dukkan garuruwan da ke kan iyaka domin samun nasara.
“Muna da kyakkyawar alaka a tsakaninmu da al’ummomin da ke iyakokin kasa . Mun gudanar da tarurruka daban-daban da al’ummomin tare da sauran humomin tsaro. A lokacin da na kama aiki a nan yankin , abin da na fara yi shi ne ziyarar dukkan sarakunan yankunan da ke karkashin kulawar ofishinmu.
“Abin da ya sa muka yi haka kuwa shi ne mun fahimci cewa akwai bukatar kyautata alaka a tsakanin jami’an tsaro da al’ummomi. Babu wata hukumar tsaro da za ta bugi kirji ta ce za ta iya yaki da matsalar tsaro ita kadai ba tare da goyon bayan al’umma ba.
“A shirye muke mu tabbatar da tsaro a kan iyaka tare da tsaftace ta daga masu yin zangon kasa ga tattalin arziki. Idan ka leka Mbok ko Yahe da sauran garuruwa na iyaka duk za ka tarar da jami’anmu a wurin” ya bayyana.
Tuni dai Shugaban NIS , CGI Isah Idris Jere ya yaba wa jami’an da suka yi nasarar cafke mutanen kana ya hore su su kara azama domin tabbatar da sauke nauyin da kasa ta dora musu.