Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NIS Ta Kafa Karin Sabbin Manyan Ofisoshi Hudu Domin Karfafa Kula Da Iyakokin Kasa

Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede ya tabbatar da kafa sabbin manyan ofisoshi na musamman guda hudu domin karfafa kula da iyakokin kasa.

Sabbin manyan ofisoshin sun hada da wanda za a kafa a Idi-Iroko da ke Jihar Ogun, da na Mfum da za a kafa a Kuros Riba, da na Jibiya da ke Jihar Katsina sai kuma na Illela da ke Jihar Sakkwato.

Shugaban na NIS Babandede ya tabbatar da kafa sabbin manyan ofisoshin ne domin cika umarnin da Ministan Cikin Gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayar na mayar da kashi 50 bisa dari na yawan jami’an hukumar zuwa sassan da ke kula da iyakokin kasa.

Sakamakon daga darajar ofisoshin, an tura manyan jami’ai masu mukaman Kwanturola domin su shugabance su, inda za su rika kai rahoton aiki ga manyan jami’ai masu mukaman Kananan Mataimakan Kwanturola Janar da ke kula da manyan ofisoshi na shiyya.

Sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta NIS, DCI Sunday ya fitar, ta yi karin hasken cewa wadannan sabbin manyan ofisoshin kari ne a kan wanda ake da shi a iyakar kasa ta Seme domin bai wa hukumar dama kara kaimin sanya ido ga mutanen da ke shige da ficen kasa domin kula da iyakoki kamar yadda ya kamata da kuma inganta tsaron kasa.

 

 

 

Exit mobile version