Ofishin Hukumar Shige da Fice na Kasa (NIS) da ke Jihar Ribas ya samar da fasfo 38,613 cikin wata biyar. Â
Hukumar ta karfafa aikace-aikacen Intanet da biyan kudi ta yanar gizo don rage cunkoso da bata lokaci a yayin neman yin fasfo.
- Gwamnatin Kano Ta Soke Lasisin Makarantun Masu Zaman Kansu A Jihar Baki Daya
- Nijar: Ba A Kone Ofishin Jakadancin Nijeriya Ba – Jakada
Dangane da bikin cika shekaru 60 na hukumar, hukumar ta samar da adadin fasfo guda 38,613 daga watan Fabrairu zuwa Yulin 2023.
Da yawa daga cikin wadanda aka yi wa fasfo ba su karba ba hakan ya sa hukumar ke amfani da wannan damar don yin kira da su je su karbi fasfo dinsu.
Kwanturola James Sunday, bayan ziyarar da ya kai ofishin fasfo, ya shawarci jami’in kula da fasfo din, Audi Maisudan mataimakin kwanturolan da ya kara kaimi wajen tuntubar juna da masu neman fasfo don samar da shi ba tare da matsala ba. a sanar da su don ba su damar warware matsalolinsu don share shari’o’in da ke kan gaba da kuma samar da fasfo.
Sannan ya bukaci wadanda suka shigar da bukatar samun fasfo musamman masu bukata da ta shafi neman lafiya zuwa kasashen ketare da su leka ofisoshin hukumar don karbar fasfo din su.
Kazalika ya jadadda kudirin hukumar ya ci gaba da inganta ayyukanta don faranta wa abokan huldarta.