Sabon dan wasan Chelsea, Christopher Nkunku, na fuskantar yiwuwar rashin taka leda na tsawon watanni.
Bayan bincike ya nuna raunin da ya ji a wasan sada zumunta da ya buga a makon da ya gabata, ya yi muni fiye da yadda ake fargaba.
- Akpabio Ya Nada Lawan, Kalu, Yari, Tambuwal Da Oshiomhole Shugabancin Kwamitioci
- Yadda Rufe Sararin Samaniyar Nijar Zai Shafi Sufurin Jiragen Sama A Yammacin Afirka
A wani babban koma baya ga Chelsea gabanin sabuwar kakar wasa, Nkunku ya samu rauni wanda zai sa a masa tiyata a gwiwa.
Dan wasan da aka sayo daga RB Leipzig kan fan miliyan 52 a bazara ya ji rauni a gwiwarsa a wani mummunan karo da dan wasan bayan Borussia Dortmund, Mats Hummels, a Chicago.
Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino, ya tabbatar da raunin amma kuma yace ba laifin filin wasan da suka buga kwallon bane kamar yada wasu ke yadawa.
Nkunku ya taka rawar gani a lokacin shirye-shiryen sabuwar kakar wasa kuma raunin da ya samu ya raunana shirin Chelsea na sabuwar kakar.
Ya zura kwallaye uku a wasanni biyar na tunkarar kakar wasa ta gaba.
Nkunku yaji raunin ne yayin karawa da Dortmund amma Pochettino ya yi fatan zai murmure cikin gaggawa.
Sai dai a yanzu Nkunku ba zai samu damar buga wasan kungiyar na farko a Firimiyar bana ba.
Wanda zasu Karbi bakuncin Liverpool ranar Lahadi, sai dai likitoci na kokarin samun cikakken tabbaci kan tsawon lokacin da zaiyi yana jinya.