Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta ayyana yau Laraba 17 ga watan Disamban, 2025, domin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan don bayyana damuwarta kan taɓarɓarewar harkar tsaro.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ga dukkanin majalisun jihohi mai ɗauke da kwanan watan ranar 10 ga watan Disamba, bayan taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), da ta gudanar a ranar 4 ga Disamba.
- Ganduje Ya Dakatar Da Shirin Kafa Hukumar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano.
- ICPC Za Ta Binciki Zargin Da Ake Yi Wa Shugaban NMDPRA
NLC ta nuna damuwa kan ƙaruwar ayyukan ’yan bindiga da sace-sacen ɗalibai a sassan ƙasar nan inda ta bayar da misali da sace ɗalibai mata da aka yi a wata makarantar kwana a Jihar Kebbi a ranar 17 ga watan Nuwamba.
Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana fushinta kan yadda aka janye jami’an tsaro daga makarantar jim kaɗan kafin kai harin, tana mai kiran lamarin da “mummunan aiki na ta’addanci” da ke buƙatar gaggawar bincike tare da gurfanar da masu hannu a ciki.
Sanarwar ta umarci dukkanin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin NLC da majalisun jihohi da su shirya tsaf tare da tattara ma’aikata da ƙungiyoyin fararen hula domin yin zanga-zangar, tana mai cewa yawaitar sace yara ’yan makaranta ya munana kuma ba za a amince da shi ba.
NLC ta kuma zargi Gwamnatin Tarayya da gazawa wajen kare makarantu, musamman waɗanda ke yankuna karkara da sauran wurare masu nisa ko masu rauni.














