Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi Allah-wadai da gazawar gwamnatin tarayya na ci gaba da biyan kudin tallafi ga ma’aikatan gwamnati na Naira 35,000 da aka fara a watan Satumba, domin rage wahalhalu da ake fama da su biyo bayan cire tallafin man fetur.
Kungiyar ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan ma’aikata kudaden rage radadin cire tallafin mai bayan ma’aikatan sun karbi na wata daya kacal.
- Matakan Amurka Na Kayyade Fitar Da Matattarar Bayanai Ta Microchip Za Su Kawo Illa Ga Kasuwar Samar Da Kayan Ta Duniya
- EFCC Ta Gurfanar Da Ma’aurata Kan Damfarar Miliyan 410 A Kano
Shugaban sashen tsare-tsare na kungiyar kwadago ta kasa Kwamred Nasiru Kabir, ya bayyana cewa sun samu takardar dakatar da biyan 35,000, kuma dama su sun fada cewa ba su amince da biyan wadannan kudade ba tun farko.
Nasir, ya ce wannan abin kunya ne gwamnati ta yi, saboda haka kungiyar kwadago ba za ta zuba ido ta ga ana zaluntar ma’aikata ba.
Ya ci gaba da cewa dama kungiyar ta dan jingine yajin aikin ne ba wai ta dage ba ne, saboda haka kungiyar tana nan daram akan bakansu babu gudu babu ja da biya.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki kan dukan kawo wuka da jami’an tsaro suka yi wa Joe Ajaero a Jihar Imo.
Wannan lamari ya sanya gwamnati neman gafarar kungiyar tare da zama a teburin sulhu.