Ƙungiyar Ƙwadago ta Nujeriya (NLC), ta gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis a gaban ofishin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tana bukatar a fara biyan ma’aikatan ƙananan hukumomi shida da ke cikin Abuja sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.
Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin NLC da ke yankin Central Area a Abuja, inda ma’aikata da dama suka hallara, ciki har da malamai da ma’aikatan lafiya.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Sin Da Birtaniya Da Su Kiyaye Tsarin Kasa Da Kasa Da Aka Kafa Bayan Yakin Duniya Na Biyu
Sun yi tattaki zuwa ofishin ministan da ke Area 11, suna rera waƙoƙin haɗin kai da sukar gwamnati, suna zargin ministan da yin watsi da jin daɗinsu.
Abin ya ɗauki zafi bayan ‘yansanda da ke tsare kofar shiga ofishin suka tare wa masu zanga-zangar hanya.
Nan take ma’aikatan suka toshe hanya gaba ɗaya, suna cewa sai Minista Wike da kansa ya fito ya yi magana da su.
Wata hatsaniya ta tashi lokacin da wani jami’i daga ma’aikatar, Lawrence Garki, ya fito domin yin magana da su, amma suka ƙi saurarensa, suna ihu da cewa “ɓarawo, ɓarawo!” suna mai jaddada cewa sai Wike kaɗai suke son gani.
Wani daga cikin masu zanga-zangar ya ce: “Ba za mu tafi ba sai Wike ya fito. Mun gaji da ƙarya da jinkiri. Mutanenmu na cikin wahala, gwamnati kuma ta yi shiru.”
Masu zanga-zangar sun kuma nemi a sauke shugabannin ƙananan hukumomi shida na Abuja, suna zarginsu da rashin damuwa da halin da ma’aikatan ke ciki.
Babbar buƙatar NLC ita ce aiwatar da biyan sabon albashi na Naira 70,000 da aka riga aka cimma yarjejeniya a kai, ga dukkanin ma’aikatan ƙananan hukumomi ciki har da malamai da ma’aikatan lafiya.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, zanga-zangar na wakana, kuma babu wani martani daga Minista Wike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp