Shari’ar da ake yi wa jagoran ƙungiyar tada ƙayar baya ta IPOB wacce da aka haramta, Mazi Nnamdi Kanu, ta ci gaba a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a, inda wanda ake tuhuma ya bayyana ba tare da lauyan sa ba, domin ya kare kansa da kansa.
A lokacin da aka kira shari’ar domin saurare, Kanu ya shiga cikin akwatin masu tuhuma (dock) ɗauke da takardu da dama, inda ya sanar da kotun cewa shi da kansa ne zai wakilci kansa. Wannan na zuwa ne bayan janyewar lauya Kanu Agabi, SAN, da tawagarsa daga ci gaba da kare shi a jiya Alhamis.
- Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
- A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’arSakkwato
Kanu ya bayyana wa kotu cewa har yanzu bai samu cikakken fayil ɗin shari’ar ba, don haka ya nemi a ɗage sauraron shari’ar domin samun damar shiri.
Alkalin kotun ya saurari ƙorafin nasa, inda ya bayyana cewa za a sanar da sabuwar rana ta gaba don ci gaba da shari’ar.
Cikakkun bayanai daga baya…













