Kamfanin mai na ƙasa (NNPC), ya ce yana tattaunawa da matatar mai ta Dangote domin sabunta yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira.
Wannan bayani na NNPC na zuwa ne bayan rahotanni da ke cewa an dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a naira, duk da cewa akwai yarjejeniya da aka ƙulla tun da farko.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]
- Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto
A wata sanarwa da NNPC ta fitar a ranar Litinin, kamfanin ya musanta wannan batu, yana mai cewa yarjejeniyar ta na nan har zuwa ƙarshen watan Maris ɗin 2025.
“Yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a naira tana tsawon wata shida, bisa sharaɗin akwai mai, kuma za ta ƙare a ƙarshen watan Maris na 2025,” in ji Olufemi Soneye a sanarwar.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa domin cimma sabuwar yarjejeniya.
Masana na gargaɗin cewa idan NNPC ta daina sayar wa matatar Dangote mai a naira, hakan na iya haifar da hauhawar farashin man fetur, maimakon rage farashin da ake tsammani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp