Kamfanin kula da albarkatun mai na kasa (NNPCL) na fuskantar matsin-lambar rage farashin litar mai, yayin da gidajen mai da hadin gwiwar matatar mai ta dangote ta sanar da dage farashin litar mai karo na farko a 2025 a ranar Litinin.
Shugaban kungiyar masu gidajen mai, Billy Gillis-Harry, da mai magana da yawun kungiyar dillalan mai a Nijeriya, Chinedu Ukadike, su ne suka bayyana hakan.
- Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Litar Mai Zuwa Naira 965 A Abuja
- Yadda Rahoton Bincike Ya Zargi NNPCL Da Karkatar Da Naira Biliyan 514
Shafin kamfanin mai na intanet ya sanar da rage farashin litar mai zuwa naira 925 a Legas, kudu maso yamma kuma na naira 933, arewa naira 945, kudu maso gabas naira 955. Sabon ragin farashin ya sauko daga naira 970 da kamfanin ke sayarwa kafin wannan ragin.
Wannan matakin na zuwa makonni da matatar man dangote ta sanar da rage farashin litar mai zuwa naira 870 daga naira 970.
Da suke tofa albarkacin bakinsu, Gillis-Harry da Ukadike sun nuna rage farashin litar mai wani mataki ne mai matukar kyau.
Gillis-Harry ya ce, “NNPC bai da wata mafita illa kawai ya rage farashin litar mai a gidajen mansa, ba zai yiwu mutane suna ganin akwai gidajen mai masu sauki kuma su je gidajen man NNPCL.”
Kazalika, Ukadike ya ce, tun da ana samun bambancin farashin litar mai a tsakanin matatar mai dangote da kamfanin NNPCL, ba abun da ya rage wa mutane fiye da su je inda za su samu sauki.
“Da yiwuwar kamfanin NNPCL zai rage farashin litar mai saboda akwai kokuwar farashin tsakaninsa da matatar man dangote. Da zarar matatar man dangote ta rage farashin litar mai, shi ma NNPC zai biyo baya,” ya shaida.
Dalilin da ke janyo ko da matatar man dangote da NNPCL sun rage farashin litar mai, jama’a ba su ganin alfanun hakan a zahirance a harkokin sufuri da sauran bangarori, kamar su bangaren abinci, Gillis-Harry, ya ce rashin karfin sayayyar ‘yan Nijeriya shi ne babban dalilin da ragin farashin bai tasiri kan sufuri da kayan abinci.
Sai dai, Ukadike ya tabbatar da cewa muddin farashin litar mai zai ci gaba da sauka, to tabbas farashin sufuri, kayayyaki da kayan abinci za su sauki.