Jam’iyyar NNPP ta maye gurbin dan takarar kujerar dan majalisar wakilai Mai wakiltar kananan hukumomin Toungo, Jada, Ganye da Mayo Belwa, Muhammad Bello, da mamba mai wakiltar mazabar Jada-Bulo a majalisar dokokin jihar, Hammatukur Yattasure.
Dama dan majalisar dokokin, shi ne shugaban masu rinjayen majalisar dokokin jihar, da magoya bayansa sun canja sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.
Da yake jawabin karban mamban a Yola, sakataren yanki na jam’iyyar Adamu Hammatukur Ribadu, yace jam’iyyar ta maye gurbin dan takarar kujerar dan majalisar wakilan ne, bisa doka, da tanadin hukumar zabe INEC.
Yace “kasan in ana kamun Kifi, in an kamo Giwan ruwa to sai gidan Sarki, to wannan kamun da mukayi, yasa muka kira wanda ya tsaya mana takara a kananan hukumomin Ganye, Jada Toungo da Mayo-Belwa, mukace ga kamunda mukayi.
“Shi da kansa yace ya sauka, ya rubuta cewa ya janye masa, don haka Honarabul Yettusure kai ne dan takaranmu, a kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Ganye, Jada, Toungo da Mayo-Belwa, don ba zamu barka ka shigo NNPP ka tsaya a mamban jam’iyya kawai ba.
“Me yasa mukace kai mana takara? don mun tabbata Mayo-Belwa, Ganye, Jada, Toungo, idan Allah ya yarda kujerarka ne, wannan muna da tabbaci akai, kamar yadda muka dauki alkawari wanda ya janye maka a takara, jam’iyya kuma ta yarda ta maye gurbinsa da kai” inji Ribadu.
Da shima ke jawabi Honorabul Hammatukur Yattasure, ya gode da karamcin da jam’iyyar ta nuna masa, yace bai shigo jam’iyyar da nufin yaudara ba.
Yace “ina son in tabbatar muku, zuwana wannan jam’iyya bana yaudara bane, na zo ne domin ci gaban Adamawa, Nijeriya da yankin da na fito, idan Allah ya so ya yarda duk wani abu da zamuyi da jama’a zamuyi.
“Domin dama problem din na jama’a ne, dattabai da talakawa, su ne masu shirin, idan za ku bamu cikakken hadinkai da goyon baya da shawarwarinmu ya zama abu daya, to idan Allah ya yarda mu zamu ci zabe” inji Yattasure.
Dama dai mamba mai wakiltar mazabar Jada-bulo a majalisar dokokin kuma shugaban masu rinjayen majalisar Hammatukur Yattasure, ya fadi zaben fidda gwanin kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Ganye, Jada, Toungo da Maye Belwa, da jam’iyarsa ta PDP ta gudanar a kwanan baya.