A ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu magoya bayan jam’iyyar PDP a karamar hukumar Soba masu dimbin yawa suka koma jam’iyyar NNPP, bisa jagorancin Alhaji Salisu Mohammed Maigana, wanda kuma shi ne babban jami’in da ke kula da kungiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Soba.
Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kaduna, Alhaji Usman Danbaba, shi ne ya wakilci shugaban jam’iyyar na Kaduna, Mistake Ben Kure a wajen karbar wadanda suka canza shekar, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda fitaccen dan siyasa kuma wanda ya yi takarar majalisar Jihar Kaduna a jam’iyyar PDP tare da dandazon magoya bayansa suka dawo jam’iyyar NNPP.
Alhaji Usman ya shaida wa wadanda suka canza shekar cewa, an karbe su da hannu biyu a wannan jam’iyya ta NNPP, inda ya ce yana fatan za su zama wakilan jam’iyyar a gundumominsu wajen samun nasarar a zaben shekara ta 2023.
A jawabinsa, Sarkin Dillalan Tudun Wadan Zariya, Alhaji Ahmed Shehu wanda ya kasance jagoran Kwankwasiyya a Jihar Kaduna, kuma dan takarar majalisar Jihar Kaduna a mazabar Zariya a karkashin jam’iyyar NNPP, ya bayyana canza shekar da Alhaji Salisu Mohammed Maigana tare da mgoya bayansa da cewa babbar ci gaba ne ga jam’iyyar NNPP a karamar hukumar Soba da ma Jihar Kaduna baki daya.