Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ajuji Ahmed, ya ce, jam’iyyar za ta ci gaba da riƙe Jihar Kano kuma tana da ƙwarin gwiwar lashe aƙalla jihohi uku na arewa a babban zaɓen 2027, duk da ficewar wasu masu riƙe da madafun iko daga jam’iyyar kwanan nan.
Bayanin Ahmed ya biyo bayan ficewar ‘yan majalisar wakilai biyu na NNPP, Abdulmumin Jibrin da Sagir Koki, waɗanda suka sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.
- Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
- Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
NNPP ta fuskanci jerin ficewar ‘yan jam’iyyar a cikin ‘yan watannin nan, ciki har da Kabiru Usman da Abdullahi Sani daga Jihar Kano, da kuma ‘yan jam’iyyar daga Jigawa, duk sun koma APC tun a watan Mayu.
Da yake magana da manema labarai, Ahmed ya ce ficewar ba za ta raunana jam’iyyar ba, amma dai, ya yi fatan alheri ga ‘yan jam’iyyar da suka fice.
Ahmed ya ƙara da cewa, NNPP tana da ƙwarin gwiwar riƙe Kano da kuma lasheh kujera a Jigawa, Kaduna, da sauran jihohi. Ya kuma yi ikirarin cewa, an ƙwace nasarar da jam’iyyar ta samu ne a Taraba a zaben da ya gabata wanda ke nuna yiwuwar samun nasara a shekarar 2027.














