Kamfanin wayoyin hannu na Nokia na shirin sallamar ma’aikatansa da adadinsu ya kama daga dubu 9 zuwa dubu 14.
Cikin sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce zai kammala daukar matakin ne nan da zuwa karshen shekarar 2026 domin tsuke bakin aljihunsa, biyo bayan koma bayan kashi 20 cikin 100 na kudaden shigar da ya saba samu.
- Kasafin 2024: Tinubu Ya Umarci Ma’aikatu Su Rika Ba Da Rahoton Ayyukansu Duk Wata
- Kirsimati: ‘Yan Nijeriya 163,000 Suka Ci Gajiyar Tallafin Sufurin Gwamnati – Minista
Shugabannin kamfanin sun ce zuwa karshen shekarar ta 2026, su na sa ran alkinta rarar kudaden da suka kama daga euro miliyan 800 zuwa euro biliyan 1 da miliyan 200.
A halin yanzu, yawan ma’aikatan kamfanin na Nokia ya kai dubu 886 a sassan duniya, duk da rage dubban guraben ayyukan da ya rika yi tun daga shekarar 2015. Kamfanin dai ya yi tashe da zarra a shekarun baya ta yadda wayar ta yi tasiri musamman wajen iya rike caji ga masu amfani, sai dai bayan zuwan manya manyan wayoyin zamani kamfanin ya rasa kasuwa da ciniki sosai.