Noman Aya na da matukar sirri, musamman a bangaren samar da kudaden shiga duba da wannan yanayi na matsin tatattalin arziki da aka tsinci kai a ciki a fadin kasar nan, don haka akwai matukar muhimmanci mutum ya samar wa da kansa wasu hanyoyi n da zai fara.
Wannan dalilin ne ya sa lallai akwai bukatar mutane su rungumi fannin noman Aya, duba da cewa;Â hanya ce ga wanda duk ya zuba jarinsa a wannan fanni, zai iya kara wa kansa samun kudaden shiga.
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
- …Nijeriya Na Asarar Naira Biliyan 4.8 Duk Shekara Kan Rikicin Manoma Da Makiyaya -Mercy Corps
Sai dai, akasari an fi yin noman Aya a Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Katsina.
Haka zalika, wannan wani fanni ne na samar da ayyukan yi kai tsaye ko kuma wanda ba na kai tsaye ba. Sannan, Aya na taimawa wajen inganta lafiyar jikin dan’adam da kara karfafa kashin jikinsa tare kuma da daidaita sigan da ke jikinsa da sauran makamantansu.
A cewar hukumar bincike da bunkasa harkokin noma ta kasa (RMRDC), Nijeriya na samun kimanin Naira biliyan 20 a duk shekara a noman Aya.
Bugu da kari, ana girbin Aya ne sau biyu a duk shekara, sannan kuma ana shukata a watan Afirilu, inda ake girbe ta kuma a watan Nuwamba.
Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, Aya na taimakawa kiwon lafiyar dan’adam, sannan kuma tana dauke da sinadarin bitamin E da C, wadanda ke taimakawa wajen kare bil’adama daga kamuwa da cututtuka.