Biyo bayan hadakar da aka kulla tsakanin wani kamfani na Kasar Saudiyya da Gwamnatin Jihar Jigawa, za a samar da sauyin noman Dabino a jihar.
An kulla wannan yarjejniyar ne tsakanin gwamnatin jihar da kuma kamfanin Saudiyyan, domin kara habaka noman Dabino a jihar.
- An Bude Cibiyar Tattarawa Da Yada Labarai Ta Taruka Biyu Na Sin
- Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe
Ta hanyar hadakar, za a yi amfani da fasahar kimiyya don samar da girbinsa mai dimbin yawa tare da samar da nau’ukansa da dama.
A cewar wasu bayanai da Hukumar Kula da Samar da Wadatccen Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, Kasar Saudiyya ita ce ta biyu da ke kan gaba wajen noman Dabibo, domin kuwa tana samar da tan miliyan 1.61.
Kazalika, kasar Masar ita ce a kan gaba wajen noman Dabino a fadin duniya baki-daya, ganin cewa a shekarar 2022 kadai, ta noma Dabino kimanin tan miliyan 1.73.
Ita kuwa Kasar Algeria, ita ce ta uku; inda ta noma Dabino kimanin tan miliyan 1.25.
Hadakar tsakanin Gwamnatin Jigawa da Saudiyya da kuma wani kamfanin aikin noma da ke kasar nan, wato ‘Netay Agro-Tech’, za ta kara taimakawa wajen sake habaka noman Dabinon a jihar.
A duk shekara, Nijeriya na noma Dabino kimanin tan 21,000, inda Jigawa ta kasance daga cikin jeren masu noman nasa.
A jawabinsa a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse, a lokacin da ya karbi tawagar wata babbar gona da ke Kasar Saudiyya, wadda ta kware wajen noman Dabino tare da ba shi kulawar da ta dace, gwamnan jihar, Umar Namadi ya bayyana cewa, sabuwar hadakar za ta bude sabon babi ga noman Dabino a Jigawa.
Namadi ya kuma ba su tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta bayar da goyon bayan cimma burin shirin, inda ya ce, hadakar ta yi daidai da kudurin gwamnatinsa na bunkasa aikin noma a jihar.
“Muna maraba da zuwan ku Jihar Jigawa, sannan kuma a shirye muke mu yi aiki tare da ku duba da cewa, al’ummar jihar za su amfana da wannan hadaka, kuma hadakar za ta taimaka wa Jigawa a bangaren noman Alkama.”
Ya bayar da tabbacin gwamnatinsa, kan samar da dukkanin kayan da ake bukata, domin tabbatar da an wazar da aikin.
Jagoran tawagar, Abdul’aziz Abdurrahman-Al-Awf, ya jaddada goyon bayan kamfanin, ta hanyar amfani da fasahar kimiyyar aikin noma, don habaka noman Dabino a jihar.
“Za mu tabbatar da cewa, an yi noman Dabino sau biyu a shekara, sannan kuma za mu tabbatar da mun horas da matasa a fannin, domin bai wa matasa horo na musamman”, in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp