Manoman kankana a jihar Jigawa na sa ran samun riba mai yawa saboda yadda ta yi kyau a bana.
A kowace shekara, a lokacin sanyi manoman na kankana a jihar Jigawa suke dibanta tare da sayar da ita a sassa daban-daban na kasar nan, har ma da wasu kasashen da ke makwabtaka da jihar.
- Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 14 Zai Gudana Ranar Talata
- Karin Bayani Kan Harin Bom Din Da Ya Kashe Fulani 39 A Nasarawa — Ganau
Daya daga cikin manoman na kankana a jihar, mai suna Muhammad Afno wanda ya fito daga karamar hukumar Guri, ya bayyana cewa, ya sayar da kankanar mai yawa a bana, ya kuma samu riba mai yawa.
 Muhammad Afno ya ci gaba da cewa, ya sayar da kowace kankanar daya a kan naira 40,000.
A cewar Muhammad, ya shafe shekaru yana yin noman na kankana, wanda har ya yi auri mata biyu ya haifi ‘ya’ya goma, wadanda dukkaninsu yake ci gaba daukar dawainiyarsu ta hanyar wannan sana’ar.
 .Muhammad ya ci gaba da cewa, akasari yana kai kankanar ce zuwa kasar Afrika ta Kudu da kuma wasu sassa na kudancin kasar nan domin sayar da ita.
Sai dai, Muhammad ya kola kan yadda rashin farashin man fetur a kasar nan ke zamo wa sana’ar ta sa kalubale wajen safarar ta.
Har ila yau, sauran manoman ta a yankin sun bayyana cewa, biyo bayan annobar ambaliyar ruwa da aka samu a kakar noman bara a yankin, hakan ya sa sun kara mayar da hankali wajen yin nomanta da rani.
.Shi ma wani manominta mai suna IbrahimTakazza ya sanar da cewa, ana samun riba mai yawa a nomanta, musamman a lokacin sanyi.
Bugu da kari, wani manominta mai suna Alhaji Ibrahim Mai Kolawa ya bayyana cewa, bayan da ya sayar da ita ya samu rubin kudaden da ya kashe wajen nomanta.
Haka kuma, a yankin Karnaya da ke cikin karamar hukumar Dutse, akasarin manoman na kankana a yankin sun bayyana cewa, sun yi girbinta mai dimbin yawa tare da samun riba mai yawa, sabanin a shekarun baya.
An ruwaito cewa, kankana ta fi yin saurin girma a dausayin noma mai kyau domin kashi 90 a cikin dari na kankana ruwa ne, inda hakan ya sa take jima wa ba ta lalace ba.