A halin yanzu Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta samu nasarar bankado ayyukan wau bata-gari da ke yi wa shirin na rage cunkoso a tashar jiragen ruwa na Apapa zagon kasa.
Shirin da ake kira ‘E-call’ ko kuma ‘Eto’ bata-garin na amfani ne da lambobin mota na jabu ne gurbata yadda NPA ta shirya nata tsarin don amfanin kansu. A watan Fabrairu na shekarar 2021 ne hukumar NPA ta kirkiro da shirin don ta rage yadda manyan motoci da ke mu’amala da tashoshin jiragen ruwa suke haifar da cunkoso a hanyoyin shiga da fita tashar ruwa na Apapa.
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
- Bai Kamata Gwamnatin Kano Ta Ɗauki Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi Ta Gina Gadoji A Birni Ba -Hikima
Sanarwar da ta fito daga hukumar NPA ta bayyana cewa, an samu nasarar dakile ayyukan masu zagon kasan ne a daidai kofar shiga ta ‘MPS’ Apapa, inda daga nan ne suke samar da tikitin da suke ba motocin na jabu wanda kuma hakan ke yi wa na gwamnati zagon kasa tare da nakasa kudaden shigar da ya kamata hukumar ta samu.
Sanarwa ta kuma ce an kama lambobin motoci 249 na jabu tare da takardar lika wa moto (Stiker) guda 282 a samamen da aka kai maboyarsu, an kuma samu nasarar kama lambobin mota 164 na jabu da ba a kai ga likawa motoci ba da kuma ‘Stika’ na likwa motoci guda 133. A nan take jami’an hukumar da kuma jami’an staron da suka jagoranci aikin samamen suka kama dukkan kayan da bata-garin ke aiki da su aka kuma nemi shugaban tashar ya kai kansa ofishin jami’an tsaro don amsa tambayoyi.
Haka kuma sanarwa ta kara da cewa, wannan ya tabbatar da matsayar hukumar na cewa, a kwai wasu bata-gari da suke yi wa shirin ‘electronic call-up system’ ta aka kirkiro don amfani da fasahar zamani wajen tafiyar da motocin da ke hulda da NPA zagon kasa.
Daga na kuma NPA ta yi alkawarin ci gaba da amfani da tsarin ‘e-call’ da sauran tsare-tsare na bunkasa tashoshin jiragen ruwan Nijeriya ta yadda za ta bayar da ciakken gudummwar da ya kamata ta bayar ga bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.