Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA da sauran masu ruwa da tsaki a fannin tafiyar da Jiragen Ruwa na kasar nan, sun yi kira da samar da tsararan tsare-tsare domin a dakile zubar da baraguzan Jiragen Ruwa a cikin Tekunan kasar.
A cewar Hukumar, yin hakan zai bayar da damar samar da kariya ga Tekunan kasar daga gurbatar da su.
- Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
- ’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3
Sun yi wannan kiran ne, a ranar Alhmis a jihar Legas a taron 2025 na ‘yan jarida maruba rahotannin ayyukan Tashoshin Jaren Ruwa na kasar
Kazalika, sun koka da cewa, duba irin wadannan baraguzan a cikin Tekunan kasar na janyo gurbatar Tekunan da shafar kiwon lafiya jama’a da sauransu.
A jawabinsa a wajen taron Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, baraguzan, na kuma haifar da tarnaki ga rauwar dabbobin halitta kamar su Kifi da ke rayuwa a cikin Tekunan.
Dantsoho wanda ya samu wakilicin Babban Manajan a Hukumar ta NPA Femi Oyewole, ya bayyana cewa, Shugaban Hukumar ta NPA, Hukumar ta mayar da hankali wajen ganin cewa, ana kare kimar Tekunan kasar.
“Hadurran zuba baraguzan kusan a kurkusa suke, wanda kuma, suke ci gaba da karuwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai matukar bukatar a dakile yadda ake duba baragunzan, a cikin Tekunan, baki daya,” Inji Dantsoho.
Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA bata yi kasa a guiwa ba, wajen daukar matakan da suka kamata, domin magance wannan matsalar.
“Duba da cewa, muna gudanar da ayyukan NPA yadda ya kamata da kuma bin ka;idojin da ke tafiyar da Hukumar, musamman wajen bai wa kayan Hukumar da ke a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar kariya, kamar yadda suka kasance a matakin na kasa da kasa na dakile gurbatar da Jiragen Ruwa ke janyo wa, musamman duba da kundin tsari na (MARPOL 73/78), za mu ci gaba da lalubo da mafita kan zubar baraguzai a Tekunan kasar,” A cewarsa.
Shugaban ya kara da cewa, kayan aikin NPA na bukatar a samar masu kariyar da kamata, musamman ta hanyar bai wa Jiragen ruwa da ke tsayawa a Tashoshin kariyar da ta kamata.
Dantsoho ya bayyana cewa, NPA akai-akai ta kan tabbatar da ana ci gaba da tsaftace Tekunan daga kalubalen baraguzan da duk wata bola, da ake zubawa a cikin Tekunan kasar a daukacin Tashohin Jiragen Ruwan kasar.
Shugaban ya yi nuni da cewa, ta hanyar kwashe baraguzan da sauran bolar robobin da ake zubawar a cikin Tekunan ne, kadai, za a iya kare rayuwar dabbobin da ke rayuwa a cikin Tekunan tare da kuma samar wa Jiragen Ruwan saukin yin zirga-zirga a kan Tekunan kasar.
Shi kuwa a na sa jawabin a wajen taron Babab Sakataren Cibiyar kungiyar masu fito kaya a Jiragen Ruwa na kasa Dakta Pius Akutah, yabawa kungiyar ta wakilan masu wallafa rahotanin a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar kan zabo wannan maudu’in domin a tattauna a kansa
Ya kuma jaddda bukatar da a tabbatar da ana tsaftace hanyoyin Ruwa da ke a Tekunan kasar, musamman domin Jiragen Ruwan da ke hawansu, su samu saukin tafiya akai ba tare da wata tangarda ba.
Akutah, wanda Mataimakin Darakata a sashen sanya ido na cibiyar ya wakilce shi a wajen taron Adeshina Sarumi, ya yi nuni da cewa, samun baraguzan a hanyoyin Ruwan na haifar da cikas ga zirga-zirgar Jiragen Ruwan.
Shi kuwa Manajin Darakta na Hukumar NIWA Bolaji Oyebamiji, ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin da su yi dukkan mai yuwa, domin a dakile wannan kalubalen da ake fuskanta, musaman ta hanyar wyar da kan alummar da ke da zama a daura da Tekunan kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp