Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, NPA, Mohammed Bello Koko, ya gargadi masu jibge manyan-manayn kwantaina a kan hanyar shiga tashar jiragen ruwa na Legas, yana mai cewa, hukumar za ta hukunta duk wanda aka kama yana aikata wannan laifi ba tare da tausayawa ba.
Shugaban na NPA ya bayyana haka ne a ziyarar bazata da ya kai tashar jiragen ruwa na Tincan Island, a ziyarar ya zagaya don ganin yadda aka shiya wuraren jibge kwantaina da kuma hanyar da aka gina don manyan motoci su ji dadin zirga zirga. Ya ce, motar da aka kama ta karya doka za a cire sunanta daga tsarin ‘Electronic Call-up System (Eto), wanda kamfanin ‘Truck Transit Park (TTP) limited’ ke gudanarwa. A ziyarar Koko ya kuma sanar da cewa, hukumar tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya ta fito da tsarin ‘Standard Operating Procedure (SOP)’ ne don ya zama abin da masu hulda da NPA za su yi amfani da shi don gudanar da ayyukansu.
- Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Wucin Gadi Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila
- Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Uruguay
Ya kara da cewa, an samar da wadanna matakan ne don inganta ayyuka da kuma karfafa wa masu hulda da tashoshin jiragen ryuwan Nijeriya, NPA.