Manajin Darakta na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA) ta sanar da cewa, Dakta Abubakar Dantsoho Hukumar ta tara Naira biliyan 758.
Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana haka ne, a ranar Laraba, a yayin da ya gabatarwa da kwamtin hadaka na kudi na Majalisar kasa, kokarin da Hukumar ta yi, a 2024.
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
- Sabon Albishir Ga Masu Kawo Ziyara Ko Yada Zango A Birnin Beijing Na Kasar Sin
Manajin Darakatan ya sanar da cewa, Hukumar ta samun nasarar tara wadannan kudaden shigar ne, daga watan Janairu zuwa watan Nuwambar 2024.
Dantsoho ya kuma shedawa kwamtin cewa, Hukumar na sa ran tara kudin shiga, da suka kai Naira biliyan 997 a 2025.
Sai dai, kwamitin wanda Sanata Sani Musa da Hon. James Faleke, ke jagoranta, ya kara yawan kudaden shigar da Hukumar take sa ran Tarawa a 2025, zuwa Naira 1.75.
Kwamtin ya bayyana cewa, ya yanke wannan shawarar ce, duba da kashi 56 na kudin shiga da Hukumar ta tara.