Shugaban Hukumar Tashar Jiragen Ruwa ta Kasa NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, Hukumar ta amfana da kasuwanci ta Afirka wadda hakan ya sanya ake sa ran samun karuwar hada-hadar kasuwanci a tsakaninta da kasashen Afirka wato (AfCFTA).
Dantsoho wanda ya bayyana haka a taron da Cibiyar Kasuwanci ta NBCC ta gudanar a jihar Legas ya sanar da cewa, wannan amfanar da Hukumar ta yi, na daga cikin kokarin ganin an tabatar da karuwar hada-hadar kasuwancin.
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
- Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya
Ya bayyana cewa, Hukumar na yin amfani da wadannan matakan, musaman domin ta saita Tashoshin Jiragen Ruwan kasar yadda suka kamata, musamman domin ta kara bunkasa dabarunta wanda hakan zai ba ta damar shiga gaban sauran takwarorinta na Tashoshin Jiragen Ruwa.
Taken taron shi ne: “Kara bunakasa gasa a tsakanin Tashoshin Jiragen Ruwa.”
“Burin mu shi ne, Nijeriya ta amfana da dabarun na AFCFTA, domin bisa maganar gaskiya Tashoshin Jiragen Ruwa na bayar da gagarumar gudunmawa wajen wajen sauke kaya na kasa da kasa.” Inji Dantsoho.
Ya ci gaba da cewa, samar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwa na kara taimakawa wajen gudanar da ayykuan kasuwanci da samar da dabaru na dogon zanago.
“ Zuba hannun jari a bangaren da ake sauke kaya a Tashohin Jiragen Ruwa da kara fadada hanyoyin layin Jiragen kasa, za su iya taimakawa wajen bunkasa aiki da kuma kara sanya gasa a ayyukan tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwa. A cewar Dantsoho
Ya sanar da cewa, samar da kyakaywan yanayin kasuwanci a kasar nan na da alaka da kokari da kuma yanayin gasar da aka samar na kasa a Tashishin Jiragen Ruwan, inda ya yi nuni da cewa, wadannan abubuwan sun taimaka wajen samun musayar kudade, daidaita tattalin ardikin kasar, kara habaka kauswanci da kuma samun masu zuwa zuba hannun jari.
Dantsoho ya godewa Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Ruwa Adegboyega Oyetola, bisa goyon bayan ada yake ci gaba da bai wa Hukumar, musamman domin a kara saita Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
Ya yi nuni da cewa, hadakar da NPA ta yi da Kungiyar kasa da kasa ta IMO za ta taimaka wajen cimma burin wannan aikin da aka sanya a gaba.
Da yake yin tsokaci kan tsarin zamanai da Hukumar ta kirkiro da shi na shigar manyan motoci cikin Tashoshin Jaregn Ruwan kasar Shugaban ya bayyana cewa, akwai hadaka a tsakanin aikin da ake gudanarwa a Tashar Jiragen Ruwa da kuma wanda ake gudanarwa a a wajen kwashe kayana da aka shigo da su ta Tashoshin Jiragen Ruwa.
A cewarsa, ana yin hakan ne, musamman domin a tabbatar da na rage cunkoso a cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, wanda hakan ya sanya Hukumar ta janyo kamfanin Messrs, domin gudanar da wannan aikin.
Ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu sama da manyan motoci 70,000 ne, suka yi rijista da wannan kamfanin na Messrs.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp