Hukumar da ke shirya gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) ta hukunta Kano Pillars FC da tarar Naira miliyan ₦9.5, tare da rage musu maki uku da ƙwallaye uku, bayan magoya bayansu sun kutsa cikin fili a yayin wasan da suka buga da Shooting Stars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano. Hakan ya sa NPFL ta rufe filin wasan tare da umartar cewa Pillars za ta ci gaba da buga wasanninta na gida a filin Muhammad Dikko a Katsina.
A cewar NPFL, hukuncin ya fito ne bisa dokar C1.1, wadda ke hukunta hare-haren da ake kai wa tawagar baƙi da jami’an wasa. Hukumar ta ce wannan mataki yana nufin tabbatar da tsabtace filayen wasa daga tashin hankali da rashin ladabi daga magoya baya. “Za mu zartas da dokoki duk lokacin da irin wannan hali ya faru,” in ji Davidson Owumi, shugaban aiyuka na NPFL.
- Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana
- Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa
An ci tarar Pillars ₦1m saboda gazawa wajen samar da tsaro, da ₦1m saboda rashin shawo kan magoya baya, da ₦1m saboda jifa a cikin fili da abubuwa masu haɗari, da ₦2m saboda kai hari ga ƴan wasan Shooting Stars da jami’an wasa. Haka kuma, Pillars za ta biya ₦2m a matsayin diyya ga ƴan wasan Shooting Stars da ₦1.5m don jami’an wasa da suka ji rauni.
NPFL ta kuma nemi hukumar ƙwallon kafa ta Nijeriya (NFF) da ta sake duba cancantar wasu jami’an wasa daga wasannin Pillars da Shooting Stars, da na Nasarawa United da Rangers. Duk da haka, Kano Pillars na da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin, sai dai za a iya ƙara musu wani hukuncin idan ba su yi nasara ba.