Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya reshen jihar Kano, sun cafke wasu barayi shida da ake zargi da barnatarwa da kuma sace kayan wutar lantarki a unguwar Hayin Da’e da ke Hotoro a karamar hukumar Tarauni ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Abdullahi ya fitar a ranar Talata.
Abdullahi ya ce, cafke wadanda ake zargin ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da ‘yan banga da ke aiki yankin suka samu.
“Hukumar NSCDC ta kama wadanda ake zargin tare da wayoyin wutar tiransifoma da ake kyautata zaton sato su aka yi a tsakar dare a yankin,” in ji shi













