Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC reshen Jihar Kano sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da sata da kuma ɓarnatar da kayan jama’a.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da wani mutum mai shekaru 35, Murtala Aliyu Muhd, daga Dawakin Dakata a ƙaramar hukumar Nassarawa, wanda ake tuhuma da satar batirin makamashin Sola daga masallacin Juma’a na Dakata.
- Takaddamar Rarara Da Hukumar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano: A Ina Gizo Ke Sakar?
- Assha: Ɓata Gari Sun Bankawa Motoci 10 Wuta A Filato
Bisa ga bayanan kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, an ce wanda ake zargin ya shiga masallacin ta taga da daddare ya ɗauke batirin na masallacin. An kama shi washegari a wani shingen tsaro a kusa da Yankaba yayin da yake ƙoƙarin kai batirin kasuwa. Bugu da ƙari, bincike ya gano cewa ya taɓa satar ₦300,000 daga masallacin a wani lokaci da ya gabata.
A wani lamari daban, an kama wani matashi mai shekaru 19, Musbahu Sani, daga Darmanawa, da manyan igiyoyin wutar lantarki da ake zargin ya sato daga wata na’urar wutar lantarki (transformer). An kama shi a kan titin Court Road, Gyadi-Gyadi, yayin da yake ƙoƙarin kai kayan kasuwa. Kakakin NSCDC ya bayyana cewa duka waɗanda ake zargin sun miƙa wa sashen shari’a na hukumar domin fuskantar hukunci.