Kwanakin baya hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta bayyana cewar ta maka mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara a wata kotun majistare da ke Nomansland a birnin Kano inda ta ke tuhumarsa da karya dokar hukumar ta hanyar fitar da wata wakarsa ba tare da ya gabatar da ita gaban hukumar domin tacewa ba.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aika wa manema labarai ya ce hukumar tace fina-finai ta aikawa da mawakin sakon korafi dangane da sabuwar wakar da ya saki ba tare da ya kawo an tace ba sai dai mawakin bai bata amsa dangane da korafin data aika mashi ba wanda hakan ne dalilin da yasa hukumar ta garzaya gaban kotun domin kowa zaman doka yake a cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar.
- Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Sasanta Batun Nukiliyar Iran A Siyasance
- Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron G20 A Kasar Brazil
Wakilin hukumar a kotu ya tabbatar da cewa tuni kotun ta aika wa mawakin takardar gayyatar sammaci sai dai ba’a ga fuskarsa ba a ranar 13 ga watan nuwamba a yayin zaman kotun ba.
Tun kafin wannan lokacin bayan sakin sabuwar wakar hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta turawa mawakin sakon neman ba’asi ta hanyar sakon kar-ta-kwana sai dai har kawo wannan lokaci mawakin bai maidowa da hukumar amsar sakon ba.
Kamar yadda kowa ya sani ne tace fina-finai, rubuce-rubuce tare da waka na daya daga cikin manyan ayyukan da suka rataya a kan hukumar domin tabbatar da tsafta tare da dora komai a bisa doron doka da oda inji shi.
Daya daga cikin makusantan Dauda Kahutu Rarara Abdullahi Al Hikma da ya ke mayar da martani a kan ikirarin da hukumar Tace Fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta yi, ya ce ko alama maigidan na sa bai san da wannan umarni da kotu ta bayar ba domin kuwa har yanzu babu wata takarda ta kotu da ta shiga hannun mawakin.
Al-hikma ya ce wannan takarda da muka ga tana yawo a kafafen sadarwa wacce wata hukuma a Jihar Kano ta maka mawaki Dauda Kahutu Rarara a kotu, ba a hukumance aka gabatar da ita ba,kuma mun san idan ana karar mutum to za a kai takarda ta sammaci a gidan sa ko wani waje da za a same shi.
Amma ba a yi ko daya daga cikin wadannan biyu ba sai dai kawai muka ji wai an kai Rarara kotu,kuma a sanarwar da aka bayar a soshiyal midiya,mu ba mu ga an ce ga kotun da ake neman mu ba kokuma ga ma wakar da aka yi inji shi.
Ya kara da cewar na ji wani da yake magana da yawun hukumar Tace Fina Finai ma ya kasa fadar sunan wacce waka ce,kuma mun yi wakoki da yawa a wannan wata wadanda aka sake su saboda haka idan har da gaske yake ya kamata ya fito ya bayyana wacce waka ce.
Kuma mu masu bin doka da oda ne munsan cewar babu wanda ya fi karfin kotu saboda haka zamu mutunta umarnin kotu idan muka samu wannan takardar sammacin,ko shugaban kasa ne aka ce an kai shi kotu, to dole zai san wacce kotu aka kai shi, kuma a kan wanne laifi ake neman sa.
To kuma mu ma ‘yan kasa ne masu biyayya ga dokokin kasa saboda haka mu ba ma raina kotu, kuma ba ma raina hukuma amma dai wannan takarda ta wannan sammaci da ake fada a kafar sadarwa muka ji ta inji Al Hikma.
Da yake amsa tambaya akan ko Rarara ya cigaba da yin wakoki a jahar Kano Al Hikma ya amsa da cewar,yanzu shi Dauda Kahutu Rarara ba wai yana yin wakokin sa a nan Jihar Kano ba ne,ko kuma yana yin wakokin sa a kan iya Jihar Kano,hasali ma wakokin a Abuja ake yin su.
Duk lokacin da ka ga ya zo Kano, to wani uzuri ne ya kawo shi, kuma zai yi ya gama kwana daya biyu ya fita,don haka yanzu ya bar Kano ya koma Abuja,to saboda haka ba mu san a ina aka kai wannan takarda ba, kuma har yanzu ba ta riske mu ba inda ta riske mu to za mu yi wa doka biyayya,sai mu sa lauyoyin mu su je su ji ba’asi na abin da ake tuhumar mu da shi, tunda dukkan mu a karkashin doka muke kuma babu wanda ya fi karfin doka.
A nata bangaren, hukumar ta yi martani kan ikirarin Rarara inda kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fada a sanarwar da ya fitar cewa, tun a ranar 8/11/2024 kotun mai lamba 47 da ke unguwar Noman’sland a Jihar Kano ta aika wa da mawakin takardar sammaci a ofishin sa da ke kan titin gidan Zoo a Kano.
Kuma bayan rashin samun sa kotun ta kara tura masa da sakon kar-ta-kwana ta hanyar tedt message da manhajar WhatsApp indaaka bukaci ya bayyana a gaban kotun a ranar 13/11/2024, dangane da maganar da wakilin mawakin ya yi na cewa ba a Kano mawakin ya yi wakar ba hakan ya tabbatar da cewa mawakin ya kwana da sanin laifin da hukumar take zargin ya aikata inji Sani Suleiman.
Haka kuma yana da kyau al’umma su kara fahimtar cewa matsawar dan fim, marubuci ko mawaki ya taba yin rijista da hukumar to dole ne ya bi dokokin hukumar a duk inda yake kamar yadda ya dauki alkawari a yayin da zai cike fom.
Daga karshe kakakin ya ce hukumar na da hurumi na saka ido, bayar da shawara ko hukunta duk wani aiki da ya shafi ayyukan da suka rataya a kan ta matsawar ya shigo Jihar Kano ko a ina aka yi aikin,ba lallai sai wanda akayi a cikin jihar Kano kawai ba Suleiman ya tabbatar.