Hukumar lura da Jami’o’i ta ƙasa (NUC) ta dakatar da bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu na tsawon shekara guda, tare da ƙara kuɗin neman lasisin kafa irin waɗannan jami’o’i daga Naira miliyan 5 zuwa Naira miliyan 25. Wannan dakatarwar ta fara aiki daga ranar Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025.
Shugaban NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin sake fasalta tsarin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya, tare da tabbatar da cewa sabbin jami’o’i za su iya fuskantar ƙalubalen karni na 21. Hakanan, an ƙara kuɗin siyan fom daga Naira miliyan 1 zuwa Naira miliyan 5, yayin da ake buƙatar masu neman lasisi da suka riga suka sayi fom su biya sabon kuɗin neman lasisin cikin kwanaki 30, ko su rasa damar ci gaba da neman.
- Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin
- Jerin Jami’o’i 18 Da NUC Ta Haramta Karatu Acikinsu
Har ila yau, NUC ta dakatar da dukkan aikace-aikacen suka daɗe ba tare da ci gaba ba tsawon shekaru biyu, da kuma waɗanda ke a matakin gabatar da wasiƙar niyya. Wannan dakatarwa na shekara guda zai bai wa hukumar damar nazarin aikace-aikacen da ke jiran amincewa, domin tantance ingancinsu.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da duba ƙa’idojin kafa jami’o’i masu zaman kansu don tabbatar da cewa sabbin jami’o’i za su iya biyan buƙatun ilimi a nan gaba.
Za a sanar da duk masu ruwa da tsaki da zarar an kammala nazarin sabon tsarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp