Ƙungiyar ƴan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) ta bayyana jin daɗinta kan sakin ’yan jarida biyu, Ruth Marcus da Keshia Jang na Jay 101.9 FM Jos, bayan kama su da aka yi yayin da suke rahoton jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfaesa Nentawe Yilwatda Goshwe.
Ƴan jaridar sun gamu da matsala ne bayan sun wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna taƙaddama tsakanin wani malami da jami’an tsaro a wajen jana’izar da shugaban ƙasa Bola Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati suka halarta.
- Tinubu Zai Ziyarci Jos Domin Halartar Jana’izar Mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
- Gwamna Kefas Ya Bamu Damar Ƙwatar Mulkin Taraba A 2027 – APC
Shugaban NUJ na ƙasa, Alhassan Yahya Abdullahi, ya yaba da matakin da babban darakta na hukumar DSS, Mr. Oluwatosin Ajayi, ya ɗauka na bada umarnin sakin su cikin gaggawa tare da bayar da haƙuri ga NUJ, yana mai jaddada cewa jami’an DSS su dinga bincike sosai kafin kama kowa.
A cewarsa, wannan mataki alama ce ta sauyi mai kyau a tsarin ayyukan hukumomin tsaro, inda ya bayyana cewa irin wannan gaskiya da amincewa da kuskure zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a da hukumomin tsaro.
NUJ ta kuma yi kira ga DSS da sauran hukumomin tsaro su ci gaba da mutunta haƙƙin ƴan jarida da sauran ƴan ƙasa, tana mai jaddada cewa ƴancin ƴan jarida na yin aikinsu cikin ƴanci shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp