Ƙungiyar masu dakon Man Fetur da Gas (NUPENG) ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya daga ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, domin nuna adawa da abin da ta kira tsauraran matakan kin amincewa da ƙungiyar da Kamfanin matatar Dangote ke yi.
NUPENG ta zargi kamfanin da ɗaukar direbobin da za su yi aiki da sabbin motocin CNG da aka shigo da su bisa sharaɗin cewa kada su shiga kowace ƙungiya a ɓangaren man fetur da iskar gas. Ƙungiyar ta ce hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki na Nijeriya, dokar aiki ta ƙasa, da kuma yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta ILO kan ƴancin kafa ƙungiya.
- Xi: Alakar Sin Da Rasha Ta Zama Misali Na Kyakkyawar Dangantakar Manyan Kasashe
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
Bayanin hakan ya fito ne bayan wani taro da NUPENG da ƙungiyar masu motocin ɗaukar mai (NARTO) suka yi da wakilin Dangote a ranar 23 ga Yuni, 2025, inda aka shaida musu cewa sabbin motocin za a tafiyar da su bisa wani tsari da ya ke ware ƙungiyoyin da suka riga sun wanzu. Duk ƙoƙarin da suka yi na shawo kan lamarin ta hanyar tattaunawa da hukumomin gwamnati bai haifar ɗa da mai ido ba.
Ƙungiyar ta ce ta yanke shawarar shiga yajin aiki bayan ta gaji da tattaunawa mara amfani. Ta kuma nemi haɗin kai daga sauran ƙungiyoyin kwadago kamar NLC da TUC. Haka kuma ta gargaɗi mambobinta na bangaren direbobin tankar mai da su fara neman wasu sana’o’i ko damar koyon sabbin dabaru idan ba a warware matsalar ba.
NUPENG ta kuma roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta shiga cikin lamarin domin tabbatar da bin doka da kare ƴancin ma’aikata, tana mai jaddada cewa yajin aikin ba domin jefa jama’a cikin wahala ba ne, illa kawai kare ƴancin mambobinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp