Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya jaddada buƙatar matasan Afrika su fara riƙe muƙaman jagoranci a faɗin nahiyar.
Obasanjo ya ce matasa su gane cewa ba shugabannin gobe ba ne kawai, shugabannin ne na yanzu.
- An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin
- Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5
Ya buƙaci da su yi amfani da yawansu don kawo sauyi mai ma’ana a Afrika.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron Presidential Youth Mentorship Retreat da aka gudanar a Abeokuta, Jihar Ogun, ƙarƙashin Cibiyar Ci gaban Matasa a Ɗakin Tarihi na Shugaba Olusegun Obasanjo (OOPL).
Taron ya samu halartar matasa daga sassan Nijeriya da wasu ƙasashen Afrika.
A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro.
Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?”
Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a yau.














