Ma’aikatar Turai da Harkokin Wajen Faransa tare da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Ayyukan Noma ta Duniya (IITA), sun kaddamar da wani shiri na horar da dalibai 500 kan harkokin noma a Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako da ke Danbatta a Jihar Kano.
Shirin, wani bangare ne na koyar da fasahar aikin gona da koyar da aikin noma (WATEA), wanda aka shirya shi don agaza wa mata, shi yasa kashi 80 na na masu cin gajiyar shirin ma, mata ne.
- Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Kudirin Kara Yawan Membobi Daga 360 Zuwa 366
- Makarantar Nazarin Al’adun Gargajiya Da Wayewar Kai Ta Kasar Sin Dake Athens Za Ta Habaka Musayar Al’adu
Horon, ya kunshi muhimman fannoni da suka hada da kwarewar fasaha, dabarun koyon sana’a da kuma samun tallafin kasuwan a harkar aikin gona.
An yi wannan yunkuri ne, domin wadata dalibai da kayan aikin da suka dace; don bunkasa wannan aiki na gona tare kuma da cike guraben da aka rasa na kwarewa, musamman wadanda aka gano.
A nata jawabin, Jami’ar Cibiyar Kula da Ayyukan Noma a Jihar Kano (IITA), Hajiya Munnira Jibrin ta bayyana cewa; Gwamnatin Faransa ta kudiri niyyar tallafa wa matasa wajen bunkasa sana’o’i masu matukar muhimmanci, domin samun nasara a harkar noma.
Jami’ar ta jaddada cewa, “Wannan horarwa, an samar da ita ne; don tallafa wa mata a harkokin kasuwancinsu,”.
Har ila yau, M. Ado Rabo; wakilin shugaban kungiyar ta IITA a Kano, ya bayyana aniyar shirin na samar da dogaro da kai a tsakanin matan da suka halarci taron.
“An tsara wannan shiri ne, domin horar da mata sama da maza; ta yadda ba za su dogara da kowa ba, kudirin shi ne; karfafa wa mata a wannan fanni na noma,” in ji Rabo.
Haka zalika, Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi; Dakta Yusif Ibrahim Kofar Mata, ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda shirin ya mayar da hankali a kan mata.
Ya kuma ja hankalin daliban da su yi amfani da wannan dama wajen bunkasa sana’o’insu.
“Gwargwadon yadda kuka rike kasuwancinku, gwargwadon darajar da za ku samu a cikin al’umma”, in ji Kofar mata.
AgroNigeria, ta ba da rahoton cewa; fitowar daliban na nuni da cewa, an samu hadin kai; don inganta ilimin aikin gonad a kuma tallafa wa mata a jihar.