ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kaddamar Da Cibiyar ‘Yan Jarida Ta Afirka Masu Amfani Da Harshen Hausa A Nijar

by Muhammad Bashir and Sulaiman
2 years ago
Jarida

A kokarin da ake na bunkasa ayyukan ‘yan jarida masu amfani da harshen Hausa a Nahiyar Afrika, an kaddamar da cibiyar kungiyar a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Wannan ne karo na farko da aka samar da irin wannan kungiya bisa la’akari da jajircewar da ake yi na ganin an bunkasa harsunan cikin gida musamman Hausa, wanda yake kokarin mamaye sauran harsuna a Nahiyar Afrika.

  • Majalisar Wakilai Ta Gabatar Da Kudirin Kara Yawan Membobi Daga 360 Zuwa 366
  • Rikicin Jam’iyyar NNPP Ya Kazanta A Kano

A yayin kaddamar da cibiyar kungiyar tare da kwarkwaryar zantawa da ‘yan jaridu na kasa da kasa, da sauran wakilai da suka zo daga sassa daban-daban ciki har da Nijeriya, masu ruwa da tsaki a wannan taro sun bayyana muhimmancin wannan kungiya wadda take da manufar aiwatar da aikin jarida nagartacce musamman zaburar da jama’a kan muhimmancin gina al’umma da samar da ci gaba mai dorewa.

ADVERTISEMENT

Maryam Sarki Azbin, wadda ta zama jigo wajen samar da wannan kungiya, ta ce lokaci ya yi da za a rika amfani da harshen cikin gida wajen isar da muhimman sakonni ga al’umma a duk inda suke.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Sarki Azbin ta bukaci ‘yan jarida da su kauce wa abubuwan da suke bata wa aikinsu kima a idon jama’a kamar izgilanci, da maula, da kwadayi, da bambadanci da keta mutuncin masu fada a ji.

Ta kara da cewa, kungiyar ta ‘yan jarida za ta yi dukkan mai yiwa wajen zaburar da ‘yan jaridu kan yadda za su rika amfani da harshen Hausa wajen sanar da mutane abubuwan da za su amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum.

A jawabinsa, shugaban hukumar gidan telebijin da radiyo na jamhuriyar Nijar, RTN, Abdoulaye Koulibaly ya bayyana cewa aikin jarida aiki ne da yake bukatar gaskiya da sanin makamar aiki, don haka kuskure ne ‘yan jarida suke yi wajen ba da labarai na shaci-fadi don son abin hannu wasu masu fada a ji, ko kuma nuna bangaranci yayin fitar da labarai.

Koulibali ya ce samar da wannan kungiya wata dama ce da za ta taimaka wajen magance kalubalen da ‘yan jarida suke fuskanta ta fannin gudanar da ayyukansu, musamman wajen amfani da harshe na cikin gida.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wurin sun gamsu da tsare-tsare da manufofin da aka gina kungiyar a kan su, musamman tabbatar da hadin kai da mu’amala a tsakanin ‘yan jarida na kasashe 11 da ke Nahiyar Afrika, suna masu cewa yawan da ‘yan jaridar Hausa da ake da su a Nihiyar sun isa su taka gagarumar gudunmawa wajen magance kalubalen da ake fuskanta, da kuma karfafawa masu kwarin giwa wajen ganin sun yi abin da ya dace na kyautata rayuwar al’ummar yankin.

Shi ma a nasa bangaren, ma’aikaci a hukumar telebijin a tarayyar Nijeriya (NTA), Aliyu Rabe Aliyu ya ce, babban aikin da kungiyar ‘yan jarida masu amfani da harshen Hausa za ta sa a gaba shi ne, sauya fasalin aikin jaridar gado na ‘yan ku ci ku ba mu, ya zuwa aikin jarida na samar da mafita ga tulin kalubalen da yankin yake fuskanta ta hanyar amfani da harshen da kowa yake sonsa, kuma yake amfani da shi watau harshen Hausa.

Jarida
Muhammad Bashir
+ posts Bio
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    ADC Na Zawarcin Gawuna Domin Ya Yi Wa Jam’iyyar Takarar Gwamnan Kano A 2027
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Gwamna Inuwa Yahaya Ya Tsaya Takarar Sanatan Gombe Ta Arewa
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Gwamna Yusuf Ya Amince Da Fitar Da Biliyan 21.2 Don Gyaran Manyan Matatun Ruwa Na Kano
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Ayyukan 2025
Jarida
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili
  • Sulaiman
    Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa
  • Sulaiman
    Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci
  • Sulaiman
    Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Uba Sani Ya ‘Yanta Fursunoni 97

MASU ALAKA

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili
Labarai

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya
Rahotonni

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
Kotu Da Ɗansanda

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

June 13, 2026
Next Post
‘Yan Nijeriya Miliyan 1.8 Ne Ke Fama Da Matsalar Yunwa – Hukumar FAO

‘Yan Nijeriya Miliyan 33 Na Iya Fuskantar Matsalar Rashin Abinci A 2025 —Rahoto

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

June 13, 2026
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

June 13, 2026
Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

June 13, 2026
An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

June 13, 2026
Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

June 13, 2026
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutun Biyu Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami A Adamawa

June 13, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

Kamfanin Simintin Dangote Ya Kaddamar Da Tsarin Fasahar Zamani (AI) Domin Inganta Tsaro Da Harkar Sufuri

June 13, 2026
Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga

Tsohon Kakakin Ma’aikatar Tsaro Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Ƴan Bindiga

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.