• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya Ya Shirya Bikin Murnar Cikar Sin Shekaru 74 Da Kafuwa

by CGTN Hausa
2 years ago
Kasar Sin

A kwanan nan ne, ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen waje da dama, suka gudanar da bukukuwa iri-iri, domin murnar cika shekaru 74, da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.

A wajen irin wannan bikin da ofishin jakadancin Sin dake tarayyar Najeriya ya shirya, jakadan Sin a kasar Cui Jianchun, ya yi waiwaye game da yadda Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta samu ci gaba, da nasarori a shekaru 74 da suka gabata, inda ya jaddada cewa, tun bayan da kasashen biyu suka kulla alakar jakadanci a shekara ta 1971, musamman bayan da suka daga matsayin alakar su, zuwa alakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a shekara ta 2005, ya zuwa yanzu, hadin-gwiwarsu na kan gaba sosai.

  • Sin Tana Bayar Da Babbar Gudummawa Ga Gina Al’ummar Duniya Mai Makomar Bai Daya
  • Da Dumi-dumi: Kotu Ta Kori Karar Da ADC Ke Yi Kan Gwamnan Gombe

Jakada Cui ya kara da cewa, kasar Sin na fatan yin amfani da damar gudanar da babban dandalin tattauna hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku, gami da dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, domin taimakawa ci gaban manufar raya Sin da Najeriya, wadda ake kira 5GIST, da kara habaka hadin-gwiwarsu.

Shi ma a nasa jawabin, mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Benjamin Kalu, ya taya Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin murnar cika shekaru 74 da kafuwa, inda a cewarsa, Sin babbar aminiyar hadin-gwiwa ce ga Najeriya, kuma kasashen biyu sun cimma tudun-dafawa, wajen karfafa hadin-gwiwa, a fannonin da suka shafi samar da muhimman ababen more rayuwar al’umma, da kasuwanci, da musanyar fasahohi, da al’adu da sauransu, al’amarin da ya taimaka matuka ga ci gaban rayuwar al’umma, gami da bunkasar tattalin arzikin Najeriya, da samar mata da dimbin guraban ayyukan yi, da taimakawa ci gaban sana’o’i daban-daban.

Jami’in ya ce, kasar Sin ta dade da yin kira, da a aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban-daban a duniya, da samar da ci gaba mai dorewa kuma cikin lumana, kana ta taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Daga nan sai ya bayyana fatansa, ga fadadar zumuncin kasashen biyu, da kara samar da damammaki, da alfanu ga al’ummunsu baki daya, da bayar da gudummawa ga shimfida zaman lafiya, da ci gaba a duk fadin duniya. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
BUA

Daga Gobe 2 Ga Oktoba Farashin Buhun Simintin BUA Ya Koma N3,500 - Kamfanin

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.