A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba.
Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashe ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna, da samun moriyar juna.
- Mastalar Tsaro: Jihohi Sun Kashe Naira Biliyan 214 Wajen Sayen Makamai
- Koch Usman Abdullahi Zai Jagoranci Kano Pillars A Karon Farko Bayan Dakatarwa
Kazalika, jakadan kasar Sin a Burtaniya, Zheng Zeguang ya ce, yin amfani da harajin fito a matsayin makami ya sabawa ka’idojin WTO, yana kuma yin illa sosai ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kana yana haifar da babbar illa ga moriyar dukkan bangarori, jakadan ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar bikin kaddamar ba da lamunin RMB na kasar Sin na farko kan ayyukan da ke maida hankali kan kiyaye muhalli wato green bond a birnin London.
Har ila yau, Zheng ya ce, kasar Sin tana adawa da karin harajin fito da Amurka ke shirin kakaba wa kan kasar Sin, kuma za ta dauki kwararan matakai don kare muradunta. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp